Ramadana: Sarkin Musulmi ya buƙaci al’umma su fara duba jinjirin wata a yau Talata

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Majalisar Ƙolin Shari’ar Addinin Musulunci a Nijeriya (NSCIA) ta yi kira ga al’ummar Musulmi a fadin Nijeriya da su fara duba jinjirin watan Ramadana na shekarar 1447 Hijiriyya daga bayan faduwar rana a yau Talata, 17 ga watan Fabrairu, 2026, wato daidai da 29 ga Sha’aban 1447.

A sanarwar da Babban Sakataren majalisar, Farfesa Is-haq Oloyede ya fitar, kwamitin duban wata na kasa tare da haɗin-gwiwar Hukumar kula da Yanayin Sararin Samaniyar Nijeriya (NASRDA) za su sanya ido wajen aikin tabbatar da ganin watan azumin.

Majalisar ta bayyana cewa, idan an ga jinjirin watan a daren Talata, Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar, Muhammad Sa’ad Abubakar, zai sanar da Laraba, 18 ga Fabrairu, 2026 a matsayin ranar farko ta azumin Ramadan. Idan kuwa ba a ga watan ba, Alhamis, 19 ga Fabrairu, 2026 za ta zama ranar farko ta azumin.

Baya ga batun Ramadan, NSCIA ta nuna damuwa kan abin da ta kira da ƙaruwar nuna wariya ga Musulmi da yaɗa labaran da ba su dace ba a kafafen yada labarai akan addinin.

A cewarta, Musulmi na fuskantar hare-hare daga masu tada ƙayar-baya da ‘yan bindiga, tare da zargin ana musu kallon da bai dace ba a wasu rahotanni da kafafen watsa labarai ke yaɗawa.

Har ila yau, majalisar ta bayyana cewa ta samu koke-koke kan jaddawalin zaɓe da INEC ta fitar, inda aka tsara gudanar da zaɓen shugaban kasa a lokacin Ramadana da kuma yiwuwar zaɓen gwamna a ranar Sallah, tana mai cewa lallai akwai buƙatar a sake duba jaddawalin.

Kazalika, NSCIA ta buƙaci Musulmi da su kasance masu haƙuri da tsayawa akan imaninsu, tare da amfani da watan mai alfarma wajen yin addu’o’i da gyaran hali da ƙarfafa zaman lafiya a yankunansu da ma ƙasa baki ɗaya.

By Babaji