Harin Filato: Kaduna da Delta sun kwashe ɗalibansu da ke karatu a Jos

Biyo bayan yadda ake samun hare-hare a baya-bayan nan a jihar Filato, hakan ya sanya gwamnatin Jihar Kaduna ta kwashe ‘yan asalin jihar da ke karatu a Jami’ar Jos da sauran manyan makarantu a jihohin da ke maƙwabtaka da jihar Filato.

Sakataren Hukumar Bada Tallafin Karatu ta Jihar Kaduna, Rilwan Hassan, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Alhamis, inda ya ce sun kammala kwashe ɗalibansu kaf a ƙarshen makon da ya gabata bisa umarnin Gwamnatin Jihar.

A cewar Hassan, an ɗauki wannan mataki ne gudun kada ɗaliban su maƙale a Filato duba da yadda jihar ke ta fama da ƙalubalen tsaro.

Ya bayyana cewa, ɗalibai guda 87 ne suka kwashe aka maida su gida a Juma’ar da ta gabata ƙarƙashin kulawar hukumar inda tuni aka sada su da ahalinsu.

Gwamna El-Rufai da Gwamna Okowa

Daga nan, Hassan ya ce hukumar za ta ci gaba da yin abin da ya dace a duk lokacin da aka fuskanci irin wannan ƙalubale na tsaro, tare da bai wa al’ummar Kaduna tabbacin ci gaba da tsare rayukan ‘yan jihar da ke karatu a Filato da sauran wurare.

A wata mai kama da wannan, Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta, shi ma ya bada umarnin gaggawa kan a hanzarta kwashe ɗaliban jihar masu karatu Jos sakamakon matsalolin tsaro da jihar ke fama da su, musamman ma a ‘yan kwanankin nan.

Sanarwar da babban mai taimaka wa gwamnan kan harkokin ɗalibai, Jerry Ehiwario ya fitar, ta nuna Jihar Delta ta soma kwashe ɗaliban nata daga Jos ɗin a ranar Alhamis.

Ehiwario ya ce, gwamnatin Delta ta ɗauki wannan mataki ne don tsiratar da rayuwar ‘yan asalin jihar da ke karatu a Filato daga rikice-rikicen da ke aukuwa a jihar.