Harin Filato: Gwamnati ta sake kafa dokar hana fita na sa’o’i 24 a Jos ta Arewa

Gwamnatin Jihar Filato ta sake kafa dokar hana fita na sa’o’i 24 a yankin ƙaramar hukumar Jos ta Arewa.

Bayanin sake kafa dokar na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da ta fito ta hannu Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Gwamna Simon Lalong, Dr Makut Macham, a ranar Laraba.

Gwamnatin Filato ta ɗauki wannan mataki ne biyo bayan ƙazamin harin da aka kai a ƙauyen Yelwa Zangam wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu a Talatar da ta gabata.

A cewar sanarwar, dokar hana fita na sa’o’i 24 ta soma aiki ne daga ƙarfe 4 na ranar 25 ga Agusta har illa masha Allahu.

Sanarwar ta ce kafa wannan doka ya zama wajibi duba da irin barazanar da aka yi wa rayuka da dukiyoyi a yankin ƙaramar hukumar da lamarin ya shafa, da kuma buƙatar tabbatar da jama’a sun ci gaba da bin doka da oda a yankin.

Idan dai za a iya tunawa, sama da mako guda kenan da gwamnatin jihar ta kafa makamanciyar wannan doka a yankin ƙaramar hukumar biyo bayan kashe wasu matafiya su 25 a yankin waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba.