Lalong ya yi tir da harin Jos ta Arewa

Gwamna Simon Lalong na Jihar Filato, ya yi tir da ƙazamin harin da aka kai a ƙauyen Yelwa Zangam da ke yankin Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da kuma lalata ɗimbin dukiyoyi.

Gwamnan ya bayyana harin wanda aka kai cikin daren Talatar da ta gabata a matsayin dabbanci, tare da cewa tuni jami’an tsaro sun cafke wasu mutum goma da ake zargin suna da hannun a harin.

Lalong ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa ta hannu daraktansa na yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Dr Makut Macham, a wannan Laraba.

Ya ce kama waɗanda ake zargin da aka yi wani yunƙuri ne na ƙoƙarin daƙile sauran waɗanda ke da hannu a aika-aikar da kuma ubannin gidansu don su fuskanci hukunci.

Sanarwar ta ce gwamnati ta yi matuƙar damuwa kan harin da ta ce bayanan tsaro sun nuna shiryayyen al’amari ne wanda aka tsara aka kuma aiwatar.

Haka nan cewa, yayin harin sai da aka lalata gadar da ke sadar da jama’a da yankin domin hana jami’an tsaro tsallakowa yankin a lokacin harin.

Daga nan Lalong ya jajanta wa al’ummar yankin kan wannan mummunan al’amari da ya faru da su, kana ya yi kira a gare su da a zauna da juna lafiya, tare da ba su tabbacin samun adalci.

Kazalika, ya gargaɗi miyagu da su guji aikata abin da zai cutar da jma’a, yana mai cewa duk inda suka shiga za a kamo su a kuma hukunta su komai daren daɗewa.

Ya zuwa lokacin haɗa wannan labarin, bayanai sun tabbatar da an gano gawarwaki sama da 35 na mutanen da harin ya rutsa da su.

wannan mummuna al’amari ne na zuwa ne kimanin mako guda da yi wa wasu matafiya su 25 kisan gilla a Gada-Biyu da ke hanyar Rukuba a yankin Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, ASP Gabriel Ubah ya tabbatar da aukuwar harin.