Hira da Gwamna Ortom na neman janyo wa Channels TV jangwam

Hukumar Watsa Labarai ta Ƙasa (NBC) ta aika wa tashar Channels TV ta takardar aikata ba daidai ba kan “kalaman harzuƙawa, rarrabuwan kai da rashin adalci” da Gwamnan Jihar Binuwai, Samuel Ortom ya yi, a shirin karin kumallo na tashar a ranar Talatar da ta gabata.

NBC ta bayyana haka ne a cikin wata wasiƙa da ta aike wa gidan talabijin ɗin, mai ɗauke da kwanan wata 24 ga Agusta, 2021, wadda ta samu sa hannun Babban Daraktanta, Balarabe Ilelah.

Wasiƙar ta ce, “Shirin wanda ya karɓi baƙuncin Gwamnan Jihar Binuwai, Governor Samuel Ortom, an fahimci ya ƙunshi kalaman da ka iya fusatarwa da rarrabuwar kawuna da rashin adalci wanda jagoran shirin bai hana aukuwar hakan ba.”

Wanda a cewarta hakan ya saɓa wa kundin dokokin yaɗa shirye-shirye na Nijeriya, sasshe na 1.10.4, 3.1.1, 3.3.1(b), 3.3.1(e), 3.11.1(a), da kuma 3.12.2.

Kazalika, wasiƙar ta buƙaci tashar Channels TV da ta yi bayani kan abin da zai hana ɗaukar matakin da ya dace a kanta bisa wannan saɓa ƙa’idar da ta yi. Tare da buƙatar tashar ta bada amsa a cikin sa’o’i 24 daga lokacin da ta samu wasiƙar.

Yayin shirin na ran Talata an ji Gwamna Ortom na cewa, “Shugaban Ƙasa yana ingiza ni in yi tunanin cewa abin da suke faɗa game da shi, cewa yana da wata ɓoyayyar manufa a ƙasar nan gaskiya ce saboda a bayyane yake cewa yana son mayar da ƙasar ta zama ta Fulani, amma ba shi ne Shugaban Ƙasa Bafulatani na farko ba.

“Maganar da yi game da wuraren kiwo bai yi wa Fadar Shugaban Ƙasa daɗi ba. Tun farko Fadar Shugaban Ƙasa ta aminta da batun kafa kwamitin da zai yi nazarin wuraren kiwo 368 a tsakanin jihohi 25 a faɗin ƙasa domin duba yanayin haƙƙin da kowace jiha ke da shi.

“Idan Shugaban Ƙasa mai biyaya ne ga doka, Dokar Amfani da Ƙasa ta bai wa gwamnoni damar shigewa gaba wajen yadda za a yi amfani da ƙasa a madadin talakawansu.

“Don haka wannan abin mamaki ne, kuma na yi mamakin jin haka ya fito daga bakin Shugaban Ƙasa, sai ka ce ba shi da Atoni-Janar ko kuma lauyoyi a kewaye da shi waɗanda za su shawarce shi. Ko kuma dai ya faɗi hakan ne cikin kuskure. Ya kamata ya fito ya nemi afuwar ‘yan Nijeriya.

A Larabar da ta gabata aka ji Fadar Shugaban Ƙasa ta daɗa nuna ɓacin ranta kan gwamnan, inda ta zarge shi da yin amfani da kalamai kwatankwacin kalaman da suka haifar da kisan kiyashi a Rwanda a 1994 a loakcin da yake tsokaci kan sha’anin tsaron jiharsa.

Idan dai ba a manta ba, ko a watan Mayun da ya gabata sai da NBC ta maka wa Channels TV tarar Naira miliyan 5 bisa laifin saɓa ƙa’idar aiki bayan da tashar ta karɓi baƙuncin mai magana da yawun tsegerun IPOB, a wani shirinta na siyasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *