Harin ta’addanci ya laƙume rayuka 11 a Kabul

Fashewar wani abu mai ƙarfi da ya auku ran Alhamis ya yi sanadiyar mutuwar mutum 11 a tashar jiragen saman Kabul da ke Afghanistan.

Wannan na zuwa ne ‘yan sa’o’i bayan da ƙasashen yammacin duniya suka yi gargaɗin yiwuwar samun harin ta’addanci a filin jirgin da ke ɗauke da dubban mutanen da ke ƙoƙarin ficewa daga ƙasar.

Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron Amurka, John Kirby, ya tabbatar da aukuwar fashewar, sai dai ya zuwa haɗa wannan labari ba a kai ga tantance irin irin ɓarnar da ta aukuwa ba sakamakon fashewar. Amma wani jami’in ƙungiyar Taliban ya ce mutanen da suka mutu sun kai 11.

Shugaban Amurka, John Biden ya bayyana fargabar samun irin wannan harin daga ‘yan ta’addan ISIS sakamakon yawan mutanen da ake da su a tashar jiragen masu neman ficewa daga ƙasar.