Rikicin shugabanci ya tarwatsa ƙungiyar makarantu masu zaman kansu a Jigawa

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse

Rikici ya tarwatsa ƙungiyar makarantu masu zaman kansu (NAPPS), reshen Jihar Jigawa. Hajiya Haleema Isyaku, wadda ita ce shugabar ƙungiyar a halin yanzu a jihar ta Jigawa, ta tabbatar da haka a yayin wani taro da ƙungiyar ta kira a cikin makon jiya a ɗakin taro na makarantar Al-Ni’ima Academy.

Hajiyar ta kuma ce, kafin rikicin ya nemi tarwatsa masu ƙungiyar suna da makarantu 210 da suke ƙarƙashin ikon ƙungiyarsu, amma yanzu ƙungiyar ta kasu kashi biyu kowa ya ja daga kuma sun ƙi ci gaba da gudanar da harkokinsu kamar yadda suka saba.
Sai dai kamar yadda wakilinmu ya ganewa idonsa daga cikin makarantu 210, makarantu 37 suka halacci taron da suka gudanar.

A ɓangare guda Hajiya Halima ta koka akan matsalolin ƙin biyan kuɗin makaranta da iyayen yara ba sa yi akan lokaci, ta ce hakan ba ƙaramar matsala ba ce a gare su, saboda kuɗinne suke tarawa suke biyan malamai albashin su.

Ta kuma nuna damuwarta game da halin ko’inkula da wasu iyayan suke lokacin da yaransu ba su je makaranta ba. Ta hori iyaye su saka ido akan yaransu wajen zuwan su makaranta.

Kazalika ta shawarci iyayen yaran su riqa kaiwa makarantun ziyara don ganin yadda malaman suke koyarwa tare da sanya ido akan yaran. Ta ce yin hakan zai ƙara wa malamai ƙwarin gwiwa tare da sanya ‘ya’yansu su zama yara masu hazaƙa.

Ta kuma gargaɗi ɗaukacin makarantun dake ƙarƙashin ƙungiyar ta NAPPS da su yi ƙoƙari wajen biyan kuɗin ƙungiya wato cheek up due saboda da shine ita ma ƙungiyar za ta iya gudanar da ayyukan ci gaba.

Ta ce duk makarantar da ba ta biyan waccan kuɗin ba za ta samu duk wani tallafi da ya zo jihar ba daga Gwnatin Tarayya.

Ta ƙara da cewar suna sa ran nan gaba kaɗan za a ba su tallafin kuɗi don aiwatar da gyare-gyare a makarantun daga gwamnatin tarayya, kuma duk makarantar da bata biyan babu yadda za a yi ta sami wancan tallafi.

Da ta juya wajen tsarin manhajar karatu kuma, ta ce uwar ƙungiyarsu ta kasa ta buga wasu manyan littafai da suka yi daidai da tsarin manhajar karatu na gwamnatin tarayya domin sayarwa ga makarantun, inda a ce daga yanzu uwar ƙungiyar ce za ta riƙa tsarawa ɗaukacin makarantun jarabawa a duk zangon karatu da jarabawar ƙarshe.

Ta kuma hore su da su ɗauki ayyukan ƙungiyar da muhimmanci sosai kasancewar yanzu shirye-shirye ya yi nisa na kafa bankin ƙungiyar da nufin tallafawa makarantun masu zaman kansu.

Da ta juya ta fuskar tsaro kuma, cewa ta yi sun ɗauki dukkan matakan da ya kamata na inganta tsaro a ɗaukacin makarantun da nufin kare lafiya da dukiyar malamai da ɗaliban makarantun.