El-Rufai ya yi wa majalisarsa garambawul

Daga WAKILINMU

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya sauya wasu kwamishinoni da wasu manyan jami’an gwamnati a ƙoƙarin da yake yi na kawo sababbin jini a gwamnatinsa.

Sanarwar da ta fito daga Fadar Gwamnatin jihar wadda ta sami sa hannun Mai Ba Gwamna Shawara Kan Harkokin Yaɗa Labarai, Muyiwa Adekeye, ta bayyana cikin kwamishinoni 14, an canza wa kwamishinoni takwas ma’aikatu. Kwamishinonin da ba a taɓa ba sun haɗa da: Kwamishinan Kuɗi, Kwamishinan Shari’a, Kwamishinan Gidaje da Raya Birane, Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida da kuma Kwamishinan Jin Daɗi da Walwalar Al’umma.

Sanarwar ta ƙara da cewa, Muhammad Sani Abdullahi, wanda shi ne Shugaban Ma’aikata an sauya masa muƙami zuwa Kwamishinan Ma’aikatar Kasafi na jihar.

Kwamishinonin da aka canza wa ma’aikatu sun haɗa da:

 • Ma’aikatar Muhalli: Jafaru Sani
 • Ma’aikatar Ayyuka: Thomas Gyang
 • Ma’aikatar Ilimi: Halima Lawal
 • Ma’aikatar Aayyukan Noma: Ibrahim Hussain
 • Ma’aikatar Kananan Hukumomi: Shehu Usman Muhammed
 • Ma’aikatar Kasafin Kuɗi: Muhammed Sani Abdullahi
 • Ma’aikatar Kasuwanci, Ƙirƙire-ƙirƙire da Fasaha: Kabir Mato
 • Ma’aikatar Wasanni: Idris Nyam

Sannan bayan sanya hannu a dokar kafa gundumomi a manyan biranen jihar da suka haɗa da Kaduna, Kafanchan da kuma Zariya, Malam Nasir ELrufai ya amince da naɗin waɗannan mutanen a matsayin kantomomin waɗannan gundumomin:
• Balaraba Aliyu-Inuwa a matsayin kantomar gundumar Zariya
• Muhammad Hafiz Bayero a matsayin kantomar gundumar Kaduna
• Phoebe Sukai Yayi a matsayin kantomar gundumar Kafanchan

Bugu da ƙari, Gwamnan ya amince da canza wa waɗannan mutanen sheƙa:

 • Umma Aboki, zuwa Babban Sakatariya a Ma’aikatar Kasafin Kuɗi
 • Murtala Dabo zuwa Shugaban Hukumar Kula da Yadda ake Kashe Kuɗaɗen Gwamnati
 • Abubakar Hassan zuwa Shugaban Hukumar Inshorar Lafiya
 • Tamar Nandu a matsayin Shugaban Hukumar Kasuwanni
 • Khalil Nura Khalil a matsayin Shugaban Hukumar Zuba Jari da Bunƙasa Kasuwanci
 • Maimuna Abubakar a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Muhalli
 • Amina Ladan za ta rika kula da Hukumar Kula da Hanyoyi a matsayin riƙo

Kazalika, sanarnarwar ta bayyana Farfesa Mohammed Saani a matsayin sabon shugaban Hukumar Kula da Ƙananan Hukumomi. Sai kuma Muhammed Mu’azu Muƙaddas a matsayin Shugaban Bayar da Agaji na Gaggawa da Dakta Shu’aibu a matsayin babban sakatare.