Riyad Mahraz na daf da komawa Al Ahli ta Saudiyya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Manchester city ta amince da tayin fan milyan 30 a kan ɗan wasanta Riyad Mahrez da ƙungiyar Al Ahli ta saudiyya ta yi.

Ɗan wasan mai shekara 32 tuni city ta ba shi izinin ya zauna karya shiga tawagar ’yan wasan ƙungiyar da suke atisaye a nahiyar Asia.

Yanzu haka ya rage ga Mahrez ya tattauna da Al Ahli akan batun albashin sa.

Rahotanni sun kwarmata cewa tuni ya amince da kwantaragin shekaru uku a ƙungiyar dake birnin Jeddah.

Shekaru biyu suka rage kwantaragin ɗan wasan ya ƙare a Etihad, sai dai Mahrez bayajin dadin Yadda yayi ta dumama benchi a kakar wasan da ta gabata.

Ya buga wasanni 22 kacal a gasar premier da ta gabata, haka zalika bai buga wasannin ƙarshe na gasar Zakarun Turai ba da kofin ƙalubale da city ta lashe.

Mahrez ya zo city ne daga leceicter akan kuɗi fan milyan 60 a shekarar 2018 bayan da ya taimaka wa Foxes ya lashe gasar premier League a 2016.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *