Ban ci bashin Naira biliyan 10 na CCTV ba – Ganduje

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Tsohon Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya musanta zargin cin bashin N10 biliyan domin saka kyamarorin tsaro na CCTV a Birnin Kano da kewaye.

Wani gungun ‘yan gwagwarmaya ƙarƙashin inuwar Coalition of Political Analysts Forum and Good Governane ya nemi gwamantin Abba Kabir Yusuf ta binciki tsohon gwamna bisa abin da ya yi da kuɗin.

Sai dai a martanin da ya fitar a Abuja, Dr Ganduje ya bayyana cewa bai samu zarafin karvo bashin ba saboda wata Kotun Tarayya dake Kano ta dakatar da shi bayan da Majalisar Dokoki ta amince masa.

A sanarwar da kwamishinan yaɗa labarai na gwamnatin Ganduje, Malam Muhammad Garba ya sa hannu, tsohon gwamnna ya ƙalubalanci gungun ‘yan gwagwarmayar da su kawo hujjar cewa ya karvo bashin.

Dr. Ganduje ya kuma yi zargin cewa gungun ƙungiyoyin na bogi ne waɗanda iyayen gidansu na siyasa ke ɗaukar nauyinsu domin ɓata masa suna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *