Ronaldo ya zama mafi shahara a kafar sada zumunta bayan samun mabiya biliyan ɗaya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa na duniya, Cristiano Ronaldo ya kafa sabon tarihi bayan samun jimillar mabiya biliyan ɗaya a shafukansa na sada zumunta.

Ganin haka ya sa Ronaldo yi yi godiya ga magoya bayansa tare da jinjina mu su kan soyayyar da suke nuna masa a lokacin da ya ke haskawa a fagen ƙwallo.

Ronaldo, wanda a halin yanzu ɗan wasa ne na ƙungiyar AL Nassr ta ƙasar Saudiyya, ya bayyana a shafinsa na X cewa hakan ya samu ne sakamakon soyayyar da shi da magoya bayan nasa ke wa tamola.

Ɗan wasan yana da mabiya sama da miliyan 638 a Instagram, a Facebook miliyan 170, a X (Twitter) kuma miliyan 113 yayin da kuma aka samu waɗanda suka yi rijista guda miliyan 60.7 a YouTube da sauransu.

Ya kuma tabbatar wa mabiyan cewa zai cigaba da kafa tarihi a yayin kasancewar sa a cikin filin wasa da ma wanin sa a nan gaba.

By Babaji