
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Tarayya ta sanar da ranar Litinin, 16 ga watan Satumba, 2024 a matsayin lokacin hutu ga ma’aikata don bikin zagayowar ranar Maulidin haihuwar Annabi Muhammad (SAW).
Ministan Harkokin Cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo ya faɗi hakan a madadin Gwamnatin Tarayya inda ya ce, ya na taya al’ummar musulmi na gida da waje murnar bikin.
Cikin wata takarda da Sakatariyar Ma’aikatar, Dakta Magdalene Ajani ta fitar, ta ce, Tunji-Ojo ya yi kira ga al’ummar Musulmi da ƴan Nijeriya baki ɗaya su kasance masu haƙuri da sadaukarwa.
Ya kuma yi kira gare su da su yi amfani da wannan lokaci wajen yi wa ƙasa addu’ar samun zaman lafiya da cigaba mai ɗorewa.
