
Daga BELLO A. BABAJI
Wasu daga cikin wanɗanda suka tsira daga ambaliya mafi muni da aka yi a tsawon shekaru 30 a Maidugurin Jihar Borno sun bayyana yadda suka tsira daga iftila’in.
Mamakon ruwan sama wanda aka fara a ranar Litinin da dare ya yi sanadiyar batsewar tafkin Alua wanda ya fasa wani yanki tare da haifar da ambaliya acikin garin na Maiduguri inda ya ɗaiɗaita gidaje, makarantu da asibitoci a birnin.
Sai dai, yayin da dama daga cikin mutanen yankunan suka tsira, akwai iyalai masu yawa da suka watse sakamakon ambaliyar.
Wani mai suna Abubakar Tijjani da lamarin ya rutsa da shi ya shaida wa manema labarai cewa akwai da dama daga cikin mutane da ba a gan su ba kasancewar ba a san halin da suke ciki ba kamar yadda ɗaya daga cikin magidanta ya bayyana wa manema labarai.
Haka nan, wata mai suna Jummai ta ce, an ceto iyayenta ne a Gamboru kwanaki uku bayan fara ambaliyar.
Sannan, wata mata da ba ta bayyana sunanta ba ta ce, gidanta ya na rukunin gidaje na 505 akan hanyar Dikwa inda sai da ta biya N100,000 kafin masu tuƙin jirgin ruwa su ceto mata tumakanta daga ambaliyar bayan tsira da ta yi a karon fari.
