
Daga BELLO A BABAJI
Ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya ƙarfafa matsayinsa a rikicin shugabancin jam’iyyar PDP bayan da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ya tabbatar da tawagarta mambobinta a jihar Ribas.
Baya ga nasarar haka ga ƴan ɓangaren Wike, sun kuma dakatar da zaman Majalisar Zartarwa ta Ƙasa saboda gujewa sauya hukuncin wanda da farko an shirya yin sa ne a ranar 26 ga watan Satumba inda daga bisani aka mayar da shi ranar 24 ga watan Oktoba.
Kwamitin gudanarwar ƙarƙashin jagorancin Shugaban jam’iyyar, Umar Damagum ya yi hukuncin a yayin wani zama a hedikwatar PDP da ke Flazar Wadata a Abuja, ranar Alhamis.
Tsawon makonni uku kenan da aka yi ta ɗage zaman kasancewar akwai zaman ɗar-ɗar a tsakanin tsohon gwamnan jihar, Wike da ƙungiyar gwamnonin PDP kan matsayin tawagar mambobin jam’iyyar na Ribas.
An kawo ƙarshen rikicin siyasar da ke tsakanin Wike da gwamna mai ci, Siminalayi Fubara ne a ranar 24 ga watan Agusta a lokacin da gwamnonin PDP suka shelanta goyon bayansu ga Fubara inda suka tabbatar da shi a matsayin shugaban jam’iyyar na jihar.
Hakan na zuwa ne bayan da Wike a ranar 31 ga watan Agusta ya yi iƙirarin haddasa rikici a jihohin gwamnonin matuƙar ba su daina tsoma baki a harkokin Ribas ba.
