Shekaru huɗu na shugabancin farfesa Armaya’u Hamisu Bichi a matsayin shugaban jami’ar tarayya ta Dutsinma sai san-barka

Spread the love

Daga MUHSIN TASIU YAU

Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi gudummawar da ya bayar a ɓangaren koyo da koyarwa ba za a iyakance ta ba a ƙanƙanin lokaci duba da tun da ya taso gaba ɗayan rayuwarsa tana cikin farfajiyar koyarwa a jami’a ne. Horon da ya samu ne a shekarun baya shi ya janyo waɗannan shekaru huɗun nasa suka kasance abin alfahari da tinƙaho da godiya da sambarka ga duk wanda ya tsinci kansa a ƙarƙashin mulkinsa ko a karatu a makarantar ko aiki ko ma zamanka ɗan Katsina ko mai kishin Katsina da kishin Arewa. Don kuwa duk wanda yake kishin ilimi da cigabansa yasan Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi a jami’ar Tarayya da ke Dutsim-ma lallai kwalliya ta biya kuɗin sabulu abin da ake buƙata an samu har da ƙari a waɗannan shekara huɗun.

Taƙaitaccen tarihin Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi

An haifi farfesa a garin Bichi a shekara ta 1969 ya yi makarantar firamare a garin Bichi bayan ya gama ya tafi makarantar sakandaren gwamnati a nan garin Bichi a shekarar1980 bayan ya yi shekara biyu a nan sai ya samu damar tafiya makarantar kimiyya ta Dawakin Kudu. Ya zauna a nan har zuwa 1985. Ya samu damar shiga jami’ar Bayero ta Kano inda ya karanta Applied biology . Bayan ya dawo daga bautar ƙasa sai ya ci gaba da karatunasa a jami’ar Bayero inda ya yi digiri na biyu da na uku. An ɗauke shi aiki a shekarar 1995 a matsayin assistant lecturer yana nan har Allah ya kai shi ya na zama farfesa a shekarar 2010. A shekara ta 2012 aka kai shi jami’ar tarayya ta Dutsimma domin ya taimaka wurin buɗe wannan jami’ar. Alhamdulillahi yanzu an yi shekara huɗu Farfesa Armaya’u yana rike wannan shawara.
Daga cikin kyawawan halayyar Farsesa a tattaunawa da muka yi da ɗalibai da malamai na cikar shekararsa huɗu a shugabancin wannan jami’a ga abin da suke cewa:
“Haƙiƙa samun shugaba mai hakuri da saukin kai irin na VC sai an tona duk abin da za a zo masa da shi na ɓacin rai da wuya ka gani a idonsa. Mu ƙananan ma’aikata in yana mu’amala da har mamaki muke yi don za ka rantse da wasu farfesoshi sa’anninsa yake mu’amala ba da leburorin da ke shara da goge-goge ba ne” cewar Muhammadu Rabe. Shi ma Tanimu Lawal wanda ɗalibi ne a jami’ar ya bayyana cewa” shekararsa uku a makarantar FUDMA amma in yana bayyana halayyar VC ga abokanansa sai su yi ta mamaki yadda ɗalibi zai iya zuwa gun VC in yana da matsala kuma ya saurare shi a take kuma ya magance masa. Dabi’ar da VC yake nuna musu su ɗalibai dabi’a ce ta Uba da ‘ya’yansa. Don haka su kansu malaman makarantar suke bin dukkanin ka’idoji na koyo da koyarwa ba sa wasa da haƙƙoƙinsu saboda in har VC ya kama an tauye hakkin ɗalibi to fa anan za a ga fushinsa.”
A ɓangaren malamai kuwa sun bayar da kyakkyawar sheda ta yadda Farfesa inda suke cewa “yake kula da dukkan haƙƙoƙinsu da ya shafi koyo da koyarwa sannan tunda ya zo bai yarda a ci zarafin malami ba, a kullum kuma yakan ƙarfafa musu gwiwa inda yake ba su tallafi kan dukkan abin da suka buƙata. Misali ƙaro karatu ko zuwa conference ko seminer bare kuma promotion wanda tunda ya zo a dai wannan jami’ar ba wanda ya taba kuka da an tauye shi. “Tsare-tsaren jami’ar da sauye-sauyen da ya kawo in dai har kana bibiyar jami’oin na duniya ba ma iya na Nijeriya ba za ka ga yana kamanta standard dinsu. Wannan tsari da ya kawo ya dace da tsarin ilimi na duniya wanda ga duk malamin da ke koyarwa a jami’ar FUDMA wannan abin alfahari ne a gare mu ba wai shi ba”

Samar da sababbin kwasa-kwasai

Lokacin da farfesa Armaya’u ya karɓi jami’ar FUDMA suna da faculty guda uku tare a program 20 kuma a cikin 20 ɗin guda uku ne kawai suke da full accreditation amma a wata shida na farko aka samu full accreditation a waɗannan goma sha bakwan. Wannan ya bayar da ƙwarin gwiwar buɗe sashen karatu na babban digiri. Yanzu haka PG school ɗin suna yin program sama da tamanin. Wato daga babu zuwa tamanin. Wannan babbar nasara ce. Daga faculty uku yanzu suna da sha uku daga programe 20 yanzu suna da sama da 100. Daga cikin faculty ɗin da babu aka samar da su a lokacinsa akwai faculty of Engineering da Faculty of Health sciences da faculty of law da Arabic da Islamic studies duka an samar da su a lokacinsa. A lokacin da farfesa Armaya’u ya zama VC na FUDMA ya tarar da su suna da centre kwaya ɗaya tal amma a yanzu akwai santoci da directorate sama da ishirin.

Ƙaro karatu ga malamai

A lokacin Farfesa Armaya’u malaman makarantar FUDMA sama da mutum ɗari huɗu sun tafi ƙaro karatu tsakanin digiri na biyu zuwa na uku a ciki da wajen Nijeriya.

Haƙƙin Ma’aikata

Ma’aikata da ke jami’ar FUDMA ba sa kuka da take haƙƙinsu saboda ana kula da su yadda ya kamata dukkan haƙƙinsu ana bayar da su. Dukkan haƙƙin su musamman promotion daga shigarsa ofis zuwa yanzu babu malamin da zai ce bai same shi akan kari ba a taba wuce biyu ga watan oktoba ba a yi promotion ba. Lokacin da VC Armaya’u ya shiga ofis farfesoshi huɗu ne kaf jami’ar amma a tsakanin shekara huɗu yanzu FUDMA tana da farfesa fin 20.

Gine-Gine da kayan more rayuwa

Wannan cigaban a bayyane yake a shekara huɗu an ƙawata jami’ar da gine-gine inda kowanne sashe yake zaman kansa kuma da duk abin da ake buƙata na ƙawata wuri don jin daɗin ɗalibai da malamai. An kawo wadatattun kayan aiki an zuba a waɗannan gine-gine. Wanda a ɓangaren gine-gine jami’ar FUDMA za ta iya gwada kwanji da dukkan jami’oin gwamnatin Tarayya da ke ƙasar nan. An yi sababbin ɗakunan kwanan ɗalibai kuma an inganta shi an zuba komai da ya dace don hana ɗalibai su takura.

Kimiyya da fasaha

A ɓangaren kimiyya da fasaha, jami’ar tarayya da ke Dutsima-ma ta zama zakaran gwajin dafi a ƙasa ma baki ɗaya , yadda ta bi sahun sauran takwarorinta a yau wajen amfani da ICT don tallafawa ilimi a zamanance da kuma kirkira da gwaje-gwaje da fasahar sadarwa don dai tafiya da zamani a wanan ƙarnin na 21, da kuma salon ilimin kimiyya na duniya. Wannan yana cikin ƙoƙarin Farfesa Armaya’u inda ya dage ba a iya malamai ba har ɗalibai sun rungumi wannan tsari na ICT inda komai nasu ya koma digital.

Ɗaukar ma’aikata

A shekaru huɗun Farfesa Armaya’u an dauki ma’aikata da daman gaske waɗanda wasu bayan an ɗauke su aikin an tura su ƙaro karatu saboda neman ƙwarewa sannan da dama suna cigaba da ayyukansu na koyarwa, wadanda kuma su ba aikin koyarwa za su yi (Non-acadamic) ba sun cigaba da aikinsu yadda ya kamata. Wadatattun ma’aikata da FUDMA take da su ya taimaka kwarai wajen cigaban kowanne ɓangaren a jami’ar don haka ta zama abin kwaikwayo ga sauran jami’oi sa’anninta da ma waɗanda suke gaba da ita a samuwa.

Harkokin tsaro

Da yardar Allah da kuma ƙoƙari da jajircewar shugaban jami’ar tarayya ta Dutsim-ma tsaro ya samu a jami’ar inda ya samu haɗin kan jami’an tsaro da malamai da ɗalibai inda ya umarci kowanne ɓangaren yake mu’amala da tuntuba ga kowanne ɓangare tare da bayar da goyon baya yayin da kowanne ɓangare ya bukaci hakan. Wannan haɗin kan da ya samu babban nasara ce musamman a ɓangaren tsaro.

Tabbatar da ɗa’a da tarbiyyar dalibai

Farfesa Armaya’u na nuna tarbiyya haƙƙin malamai ce bayan iyaye don haka ya sa ido sosai tare da kafa wasu dokoki a jami’ar waɗanda za su taimaka wurin tarbiyya da kare ɗaliban wurin afkawa abubuwa na assha. Ya tabbatar da kula da irin sutura da ɗalibai za su saka na mutumci da da hana shan taba da sauran kayan da suke saka maye, jan kunnen yaran kan shiga ƙungiyoyin asiri da duk wani abu na kaucewa addinai da al’adu. Misali lalata ko karuwanci .

Ɓangaren sufuri

Kafin zuwan farfesa Armaya’u jami’ar FUDMA tana fama da matsalolin sufuri inda da malaman da ɗaliban kowa yana ɗanɗana kuɗarsa kan sufuri musamman daga tsohon matsugunnin jami’a zuwa sabon matsugunninta. Zuwan Farfesa Armaya’u ya mayar da wannan matsalar tarihi a tsahon shekara hudu. An samar da motoci bas-bas kuma kowacce an samar mata da tsaro yayin da ake zirga-zirga da dalibai tsakanin ciboyoyin nazari da ke jami’ar a sabon mutsugunni ko a tsohon wuri. (New campus da old campus)

Ƙungiyoyin da ke jami’a da zaɓe na shugabanci na department

Ƙungiyoyi da yin zabe tsakanin malamai yayin zabar HOD yana da tasiri ƙwarai wurin cigaban jami’a da ɗorewar adalci don wannan damar ce me bayar da ‘yancin zaɓar cancanta. A baya shugaban jami’a ne ke da alhakin zaɓar da HOD amma zuwan Farfesa Armaya’u ya mayar malamai da ke sashe suke zabar abin da ya dace. A baya Farfesa Armaya’u ya sami FUDMA ba ta da ƙungiya ta ma’aikata amma da ya zo sai ya bayar da damar tare da ba su gudummawa suka buɗe ƙungiyoyinsu.Su malaman jami’a aka buɗe ASUU sai manyan ma’aikata na makaranta suka buɗe SANUU sai ƙanannan ma’aikata suka bude NASUU sai kuma ma’aikata na kimiyya suka buɗe nasu NAKT wannan ya taimaka kowa ya samu ɓangaren da zai zauna karkashin wata inuwa wato dai majingina.

Samun grant

Ɗaliban FUDMA saboda dama da suka samu da ingantacciyar koyarwa da samun sararin koya da suka yi cikin nutsuwa sun samu grand da daman gaske daga ciki da wajen ƙasar nan haka sun samo kyaututtuka daga kasashen waje. Misali yanzu haka akwai ɗaliba FUDMA da yake ƙasar Amurka wanda ya ciyo grand da yawa haka sun samu daga south Africa daga da dai gurare da daman gaske.

Don haka shekaru huɗun Farfesa Armaya’u Hamisu a matsayin shugaban jami’ar Tarayya ta FUDMA sai san barka.

By ukarofi