Yadda ’yan Nijeriya suka lashe zinare da tagulla a gasar Paralympics

Spread the love

‘Yar wasan ɗaga abu masu nauyi Onyinechi Mark ta yi nasarar lashe lambar zinariya a gasar wasannin Paralympics ta masu nakasa da ke gudana a Faransa.

Onyinechi ta ci zinariyar ne a ajin nauyin 61kg, inda ta ɗaga nauyin 150kg a makon da ya gabata a birnin Paris.

Ita ce ’yar wasa ta farko da ta ci wa Nijeriya zinariya a wasannin bana. Nijeriya ba ta ci kyauta ko ɗaya ba a gasar Olympics da aka kammala.

Da ma ita ce ke riƙe da tarihi a wannan ajin a duniya baki ɗaya.

Hakazalika, wata ’yar wasan Nijeriya, Flora Ugwunwa ta lashe lambar azurfa a gasar jifan mashi ta mata a gasar wasannin nakasassu ta Paralympic 2024 da ke gudana a birnin Paris.

Ugwunwa ta ƙare a mataki na biyu bayan da jifanta ya kai mita 19.26, bayan na Nurkhon Kurbanoɓa, ‘yar Uzbekistan da jifanta ya kai mita 21.12.

Nasarar Ugwunwa ya sa Nijeriya ta samu lambar yabo ta farko a ɓangaren jifan mashi na mata, wanda kuma shi ne lambar yabo ta huɗu da Nijeriya ta samu kawo yanzu a gasar.

’Yar wasan mai shekara 40 ta ci gaba da haskawa fagen wasanin, inda awo yanzu ta lashe lambobin yabo uku a jere a gasar nakasassu ta Paralympic, (bayan da ta lashe zinare biyu a Rio da Tokyo sai kuma yanzu ta samu azurfa a Paris)

Sauran ’yan wasan Nijeriya da suka samu lambobi a gasar kawo yanzu sun ne Onyinyechi Mark da Eniola Bolaji sai kuma Esther Nworgu.

By ukarofi