Rundunar sojoji ta soma bincike kan zargin kashe mai tallar kankana a Zamfara

Daga UMAR M. GOMBE

Biyo bayan zargin kashe wani mai sayar da kankana da aka yi cewa wani soja ya yi a Zamfara, Rundunar Sojoji ta Nijeriya ta ce ta soma bincike domin gano gaskiyar lamari.

Rundunar ta ce muddin ta bincika ta gano cewa zargin da aka yi ya tabbata gaskiya, za ta hukunta jami’in da ta samu da hannu cikin badaƙalar daidai da doka.

Rundunar ta bayyana haka ne cikin sanarwar da da ta fitar a Talatar da ta gabata ta hannun Daraktan Sashenta na Hulɗa da Jama’a, Brigadier General Mohammed Yerima.

A cikin wannan makon ne labari ya karaɗe intanet kan cewa wani soja ya bindige wani mai saida kankana saboda ya nemi sojan ya biya shi kuɗin kankanar da ya saye. Lamarin da aka ce ya fusata matasan yankin har ya kai ga rasa ran mutum guda.

Rundunar ta ce samun labarin aukuwar lamarin ke da wuya, shugaban runduna ta 8, Major General Usman Yusuf, ya sunkuya bincike domin tabbatar da gaskiyar abin da ya faru.

Rundunar ta ce har yanzu tana kan lalube domin zaƙulo wanda ya aikata aika-aikar.

Sai dai ta ce babu wata motarta da aka ƙona yayin hatsaniyar saɓanin abin da rahoto ya nuna.

Rundunar ta ce jami’anta masu aiki da ƙwarewa ne, don haka ba za su aikata abin da ya saɓa wa doka ba balle kuma ta muzguna wa jama’ar da aikinsu ne su ba su kariya.

Daga nan, rundunar ta bai wa al’ummar Zamfara tabbacin cewa lumana ta dawo yankin, kuma sojoji za su ci gaba da sauke nauyin da ya rataya a kansu na bai wai ƙasa da al’umma kariya.