Tsoron kamun hukuma: Nnamdi Kanu ya tsere daga Landon

Daga WAKILINMU

Rahotanni daga Tarayyar Turai sun nuna jagoran tsagerun IPOB, Nnamdi Kanu, wanda ya yi gudun neman mafaka, ya tsere daga Landan gudun kada hukuma ta kama shi.

A cewar jaridar The Will Nigeria, Kanu ya tsere ne bayan da ya samu labarin Gwamnatin Nijeriya ƙarkashin shugabancin Muhammadu Buhari, ta yinƙura domin ta kamo shi a can inda ya tafi neman mafaka.

Kimanin makonni biyu da suka gabata, Gwamnatin Nijeriya ta aike da takardar neman kama Kanu zuwa Tarayyar Turai ta Ma’aikatar Harkokin Wajen.

Samun masaniya a kan haka aka ce Kanu ya hanzarta tattara komatsansa ya bar Landan inda yake da zama na wani tsawon lokaci.

Kanu ya gudu zuwa Landan ne tun lokacin da sojoji suka yi yinƙurin cafko shi ƙarkashin shirinsu na Operation Python Dance da suka gudanar a garin su Kanu, Afara Ukwu da ke Umuahia.