Rundunar ‘yan sanda Nijeriya za ta hukunta ‘yan sandan da aka rabawa kuɗi a bidiyo

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta ce za ta hukunta jami’anta da aka nuna suna ƙarbar kuɗaɗe daga hannun wasu ‘yan ƙasar China a wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta.

A cikin bidiyon, an ga wasu ‘yan ƙasar China suna rabawa wasu jerin jami’an ‘yansanda kuɗi, lamarin dai ya janyo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta, inda ‘yan Nijeriya da dama ke nuna rashin jin daɗinsu tare da yin kira da a kawo sauyi kan yadda rundunar ke gundanar da ayyukanta.

A wata sanarwa da aka wallafa a shafin rundunar ‘yan sandan na dandalin ɗ, kakakin rundunar Muyiwa Adejobi, ya yi Allah-wadai da halin jami’an, inda ya bayyana abin da suka yi a matsayin rashin ɗa’a.

Ya ce, “Halayyar waɗannan jami’an ta saɓawa ƙa’idojin ɗa’a, da muhimman ɗabi’u na rundunar ‘yan sandan Nijeriya.”

Ya ƙara da cewa rundunar ta zuƙulo jami’an da lamarin ya shafa kuma ana shirin ɗaukar matakan ladabtarwa a kansu.

Ko da yake bai bayyana yanayin matakan da za a ɗauka kan ‘yansanda ba, Adejobi ya tabbatar wa jama’a cewa za a yi adalci.

Rundunar ta kuma gargadi mutane da ƙungiyoyi masu amfani da ‘yansanda, a matsayin masu rakiya da masu gadi da su kaucewa duk wani aiki da zai iya zubar da mutuncin jami’anta ko kuma janyo wa rundunar bacin suna

By ukarofi