
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Sufeta Janar na ‘Yan sanda, Kayode Egbetokun ya dakatar da rijistar yanar gizo ta e-CMR ga motoci a Nijeriya.
An bada umarnin hakan ne kwana ɗaya bayan rundunar ‘Yan sandan ta bada wa’adin 29 ga Yuli ga masu motoci su yi rijistar e-CMR kan Naira 5,375.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar da sanarwar bayan ƙorafe-ƙorafe daga ƴan ƙasa na cewa yin rijistar tilastawa ce ga waɗanda suka motoci.
Shugaban ƙungiyar lauyoyi kan muradun al’umma da cigaban Shari’a, John Aikpokpo Martins ya ce umarnin yin rijistar abin a ƙi amincewa da shi ne ga doka.
Sai dai, hukumar ‘Yan sandan ta ce ta dakatar da rijistar ne saboda akwai buƙatar a wayar da kan al’umma game muhimmancinsa ga tsaron motocinsu.
Adejobi, ya ce Rijistar e-CMR za ta taimaka wajen rage laifukan da suka shafi satar motoci, sannan rundunar za ta samu dukkan bayanai game da motoci a kundinsu.
Haka nan, fasahar za ta hana yin rijista sama da sau ɗaya ga motocin wanda hakan ma zai rage satar su.
Ya ƙara da cewa, yin rijistar ba hanyar samun kuɗin shiga ba ne ga hukumar, sai dai an samar da ita ne domin zamanantar da ayyukan ƴan sanda a ƙoƙarinsu na kiyaye rayuka da dokiyoyin al’ummar Nijeriya.
