
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Ƙasar Argentina da ke Kudancin Nahiyar Amurka ta lashe gasar ‘Copa America’ karo na 16 bayan doke Colombia da ta yi da ci ɗaya da nema a birnin Miami.
An dakatar da fara buga wasan na tsawon mintuna 80 bayan hayaniya ya kaure tsakanin magoya bayan ƙasashen biyu a wajen filin wasan.
Kyaftin ɗin Argentina, Lionel Messi ya ji rauni yayinda yake ƙoƙarin karɓar ƙwallo a zango na biyu wanda hakan ya sa aka sauya shi da wani ɗan wasan inda ya bar fili yana zubar da ƙwalla.
Lautaro Martinez shi ne ɗan wasan da ya zura ƙwallo a raga a zango na biyu na ƙarin lokaci wanda hakan ya yi sanadiyar nasarar ƙasar.
Jami’an shirye-shirye sun ce an fara hayaniyar ne bayan da wasu magoya baya da basu mallaki tikitin shiga ba suka yi yunƙurin shiga filin wasan wanda haka ya sa wasu da dama suka samu jinkiri wajen shiga.
An kama mutane da dama kan zargin su da hannu a tada hayaniyar yayinda aka garzaya da waɗanda suka ji raunuka asibiti.
Wannan shi ne karo na uku da Messi ya lashe babbar gasa ciki har da kofin duniya a shekarar 2022 wanda bai samu damar hakan ba bayan yunƙuri da dama, sai da ya kai shekaru 34.
