Spain ta yi nasarar lashe gasar Kofin Turai

Spread the love

Spain tayi nasarar lashe gasar turai ta 2024. Mikel Oyarzabal shine yayi nasarar jefa ƙwallo cikin ragar Ingila a mintunan ƙarshe na wasan.

Wasan dai ya ƙayatar sosai. Spain ita ta fara zura ƙwallo a ragar Ingila, yayin da ɗan wasan Chelsea cole palmer ya farke ma Ingila. Sai dai wasan an kai ruwa rana domin sai a mintuna na 86, Spain ta samu nasarar zura ƙwallo ta biyu. Wanda yasa aka tashi wasan 2-1.

Ingila ta kasance har yanzu tana neman nasara a gasar turai. Amma abun yaci tura.

By ukarofi