Ministan labarai ya marabci ƴan jaridan da aka yi garkuwa da su bayan sako su

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Ministan Labarai da Haɗin kan Ƙasa, Alhaji Mohammed Idris ya marabci ƴan jaridan da ke aiki a Kaduna da aka yi garkuwa da su a gidajensu ƙarshen makon da ya gabata.

Sanarwar ta fito ne daga mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Rabi’u Ibrahim a yayin ganawa da manema labarai a Abuja, ranar Lahadi.

A lokacin da ya ke magana yayin martabar AbdulGafar Alabelewe na jaridar ‘The Nation’ da kuma AbdulRaheem Aodu na jaridar ‘Blueprint’ daga mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu, Ministan ya jinjina wa hukumomin tsaro a ƙoƙarinsu wajen ganin an ceto ƴan jaridan.

An sako iyalai biyun ne tare da matar Alabelewe da yara biyu.

Ministan ya kuma tausaya musu tare da jinjina wa ƙoƙarinsu na ganin an ceto waɗanda aka yi garkuwa da su.

Kazalika, ya kuma yi kira ga ƴan Nijeriya su cigaba da bai wa gwamnatin shugaba Tinubu da hukumomin tsaro goyon bayan a ƙoƙarinsu na ganin an ceto waɗanda aka yi garkuwa da su ba tare biyan kuɗin fansa ba.

A lokacin da yake magana kan lamarin, Ribadu ya ce an ceto mutane biyar ɗin ne bayan wani aikin bincike na haɗin gwiwa da hukumomin tsaro suka gudanar.

By Babaji