Jam’iyyar APC ta sha kashi a hannun Jam’iyyar PDP a zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin Jihar Adamawa.
Wannan ya fito ne bayan da hukumar zaɓe ta Jihar Adamawa ta bayyana sakamakon zaɓen. Ta bayyana cewa dukkanin kujerun Jam’iyyar PDP ce ta lashe tare da kansiloli. Sai dai Jam’iyyar NNPP tayi nasarar lashe kujerar kansila ɗaya.
Hukumar ta tabbatar cikin jami’u 19, guda 12 ne kaɗai suka shiga zaɓe.
Wannan zaɓen shine na farko da akayi bayan hukuncin kotun ƙoli a kan cin gashin kai na ƙananan hukumomi.
