
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Fadar Shugaban Kasa ta ƙaryata jita-jitar cewa Mai Ba Shugaban Kasa Shawara akan Harkar Tsaro (NSA), Nuhu Ribaɗu ya yi murabus daga muƙaminsa.
Wata majiya daga fadar ta bayyana cewa Ribaɗu na cigaba da aiki kamar yadda aka saba, kuma har yanzu yana da cikakken amincewar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Rahoton ya bayyana cewa sabon naɗin Manjo Janar Adeyinka A. Famadewa (mai ritaya) a matsayin Mashawarci na Musamman kan Tsaron Cikin Gida ba nufin maye gurbin NSA ba ne, illa dai ƙarfafa tsarin tsaron ƙasa.
A cewar majiyar, sabon ofishin zai taimaka wajen inganta aikin tsaro a fannoni kamar shige da fice, Cibil Defence, tsaron sufuri da tattara bayanan sirri na cikin gida.
Majiyar ta ƙara da cewa, Ribaɗu zai cigaba da samun yardar Shugaba Tinubu kuma zai cigaba da aikin kula da lamuran tsaro ta haɗa hannu da hukumomin tsaron Nijeriya.
Fadar Shugaban Kasa ta kuma yi gargadi akan yaɗa labaran ƙarya, tana mai kira ga jama’a da su guji jita-jita da ka iya haifar da ruɗani a harkokin tsaron ƙasa.
