Daga AISHA ASAS
Fitaccen kamfanin Yash Raj Films ya saki tallan fim ɗinsa mai dogon zango ‘War 2’ ranar 20 ga Mayu, 2025, daidai da zagayowar ranar haihuwar tauraron Kudu, Jr NTR. Fim ɗin, wanda Ayan Mukerji ya jagoranta, ya haɗu da ɗimbin yabo da kuma ɗan-karan suka.
Hrithik Roshan ya dawo da rawar sa a matsayin Manjo Kabir Dhaliwal, jagoran jami’an leƙen asiri. Amma wannan karon, yana fuskantar sabon maƙiyi: Jr NTR, wanda ke bayyana a karon farko a Bollywood, cikin wani hali na girmamawa da jarumta. “Na ji daɗi sosai da samun damar fuskantar Hrithik a fim ɗaya,” inji Jr NTR.
Kiara Advani ta shigo da sabon salo a matsayin jami’ar kwamfuta mai rikitarwa. Wannan ita ce rawar ta ta farko a jerin finafinan ‘Spy Uniɓerse’. Alia Bhatt ma ta ce: “Wannan shi ne aikin Ayan mafi inganci.”
Duk da yawan kallon da tallan ta samu, sama da miliyan 48 a cikin awanni 24, wasu sun nuna rashin jin daɗinsu da tasirin hotunan kwamfuta (CGI) da kuma wani lokaci da Kiara ke cikin riga mai yanka da yawa. Wasu sun ce hakan ba ya da alaƙa da labarin fim, yayin da wasu ke ganin hakan wani ɓangare ne na salon fim ɗin leƙen asiri.
‘War 2’ ba fim ba ne kawai, wata manufa ce daga Bollywood wajen gwagwarmayar fafatawa da manyan finafinan Hollywood. Wannan fim na daga cikin ginin babban tarihin “Spy Universe” da suka haɗa da ‘Pathaan’ da ‘Tiger 3’. An shirya saki fim ɗin a duniya bakiɗaya ranar 14 ga Agusta, 2025, daidai da shagulgulan Ranar ‘Yancin Kai a Indiya.
Masoyan Hrithik da Jr NTR sun kaddamar da wata gagarumar haɗin gwiwa da taken “South-North Unity”, suna shirya kallon fim ɗin tare a sassa daban-daban na ƙasar Indiya.
