Sabuwar kasuwar dabbobi ta fara karɓar baƙuncin fatake a garin Ogere – Garkuwan Ogere

Spread the love

Daga DAUDA USMAN a Legas

Sabuwar kasuwar sayar da dabbobi wato United International Market dake garin Ogere a shiyyar ƙaramar Hukumar Remo cikin jihar Ogun ta fara karɓar baƙuncin manyan fatake ‘yan kasuwa masu kawo shanu daga Arewacin Nijeriya zuwa jihohin Kudu da Yammacin Nijeriya domin buɗe kasuwar sayar da dabbobi a ranar Lahadin nan mai zuwa.

Shuwagabannin kasuwar a ƙarƙashin jagorancin babban shugaban Alhaji Garba Salihu Garkuwan Ogere sune suka tabbatar da hakan a lokacin da suke zantawa da Jaridar Blueprint Manhaja a jihar Ogun dangane da wannan al’amari, inda babban shugaban kasuwar ta dabbobi United International Market Ogere Alhaji Garba Salihu kuma garkuwan Ogere ya fara da cewa shi da sauran shuwagabannin kasuwar sun shirya tsaf domin ganin kasuwar ta fara ci a ranar Lahadin nan mai zuwa. Ya ce kaɗan daga cikin shuwagabannin ɓangarorin kasuwar ta dabbobi sun haɗa da Sarkin Fulanin Ogere Alhaji Bammi Ilabin da sakataren kasuwar Alhaji Aliyu Idiris da Mohammed Abubakar Ogere da sauran manyan ‘yan kasuwar dabbobi makamantansu.

Ya ƙara da cewa akan haka yake shaida wa fatake masu sana’ar kasuwancin shanu na Arewacin Nijeriya masu kawowa jihohin Kudu da yammacin Nijeriya da sauran masu sana’ar ƙananun dabbobin da ake yankawa domin amfanin al’umma ka da su bari a barsu a baya  a wajen ganewa idanuwansu yadda kasuwar za ta fara ci a ranar Lahadin nan mai zuwa.

Hakazalika ya ƙara da cewa suma sauran ‘yan kasuwa masu sayar da kayayyaki na kowanne kala suna da rawar da za su taka domin amfanin kawunan junansu a ranar Lahadin mai zuwa sannan kuma ya ce za su yi iyakar ƙoƙarin su awajan tabbatar da matakan tsarọ a kasuwar da kewayenta gaba ɗaya domin ‘yan kasuwa da sauran al’umma su cigaba da gudanar da harkokin kasuwanci a cikin walwala da jin daɗi.

Haka kuma ya nemi ‘yan kasuwar da su ci gaba da gudanar da harkokin kasuwancin su a cikin tsafta tare da yin adalci domin samun kyakkyawar riba a ranar gobe kiyama.

Sauran jawaban da suka fito daga bakunan shuwagabannin kasuwar wanda suka haɗa da Sarkin Fulanin Ogere Alhaji Bammi Ilabin da sakataren kasuwar Alhaji Aliyu Idiris da Mohammed Abubakar Ogere dukkan jawabansu sun karkata ne a wajen kiraye -kiraye ga ‘yan kasuwar domin cigaba da zaman lafiya da sauran ƙabilu mazauna yankin.

By ukarofi