SERAP da Amnesty sun haɗa hannu don ceto ‘yan zanga-zangar matsin rayuwa

Spread the love

Fitattun ƙungiyoyin farar hula irinsu SERAP, Amnesty International da ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam sun yi tir da Allah wadai a kan yadda ake cigaba da tsare da masu zanga-zangar ƙuncin rayuwa da ta gudana makonnin baya da suka shuɗe.

Kwanaki Jaridar nan ta rawaito yadda ƴan sanda suka kama aƙalla mutum 100,000 sanadiyar wannan zanga-zanga.

Daga cikin waɗanda aka kama akwai yara a cikin su, kuma sun koka yadda ake musu horo da yunwa da rashin basu abinci mai gina jiki.

Ana tsaka da shari’ar wata ƙaramar yarinya ta faɗi ta suma saboda yunwa, bayan ta farfaɗo aka bata ruwa biskit.

Sai dai SERAP ta yi Allah wadai da wannan kamu, kuma ta buƙaci a gaggauta sakin duk wanda aka tsare a dalilin zanga-zangar ƙuncin rayuwa da ta gudana. SERAP ta cigaba da cewa wannan take haƙƙin ɗan Adam ne, tunda kowa na da ƴancin zanga-zanga a dimukraɗiya.

Itama ƙungiyar Amnesty International ta yi tir da wannan al’amari inda itama ta buƙaci a saki ƙananan yaran nan. Ta jaddada cewa wannan cin zarafi ne kuma take dokar dimukraɗiya ce.

Shima kodinetan Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam Emmanuel Onwubiku ya bayyana lamarin a matsayin babban laifin cin zarafin ɗan Adam kuma ya nuna cewa tabbas Nijeriya ba ta san haƙƙin yara ba.

By ukarofi