Yadda hakimai da dagattai 19 suka yi murabus a Sakkwato

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Hakimai da dagattai 19 sun ajiye rawaninsu a ƙaramar Hukumar Sabon Birni da ke Jihar Sakkwato domin shiga siyasa.

Yankunan da sarakansu suka yi murabus su ne Sabon Birnin Gabas da Tsilba da Sabon Garin Danbaki da kuma Magajin Dawakin da ɗan Faru da Zumbuli da Dawakin da Kanwuri da Hande da Sabon Fegi, Tudun Dankusu da Alhazzai da sauransu, inda suka bayyana goyon bayansu da Sanata Ibrahim Lamiɗo.

Sun yi murabus daga sarauta ne mako biyu bayan Hakimin Sabon Birni, Alhaji Abdullahi Muhammad Bawa, ya sauka daga sarautarsa a a ranar 16 ga watan Oktoba, 2024, da cewa, “Na ajiye sarauta ne domin in goyon bayan tafiyar siyasar Sanata Ibrahim Lamiɗo.”

Daya daga cikin waɗanda suka ajiye sarautar, Dagacin Taka-Tsaba Alhaji Lauwali Shuaibu, ya shaida wa manema labarai a Sakkwato cewa, “Mun miƙa takardunmu na sauka daga sarauta, amma babu wanda ya kira mu don jin ƙorafinmu.”

Ya ce sun ɗauki matakin ne bisa la’aikari da yadda Sanata Lamido ya jajirce wajen kula da jin daɗinsu da kuma “zuwa ya kawo mana ɗauki a duk lokacin da ’yan ta’adda suka kawo mana hari.

“Goyon bayanmu zai ƙarfafi Sanata Lamido ya ci gaba da kyakkyawan aikin da yake wa al’ummarmu.”

Alhaji Jamilu Gwanda Gobir, Ubandoman Sarkin Gobir, Marigayi Isa Muhammad Bawa, ya ce sun yi haka ne domin ceto yankin Gobir.

“Kimanin sarakai 10 ne suka mara min baya muka ajiye rawunnanmu kuma ni ne na riƙe sarautar Ubandoma na tsawon shekara tara,” in ji shi.

Tsohon Ubandoman ya ce sarakunan da suka ajiye kujerunsu sun yi alwashin ba za su goyi bayan wani ɗan siyasa ba, sai wanda ke kula da jin daɗin al’ummarsu.

By ukarofi