Sai da izinina za a riƙa ba wa manyan mutane ’yan sanda – Tinubu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya nanata ƙudurinsa na janye ’yan sanda daga gadin manyan mutane a ƙasar, inda ya ce janyewar ta zama tilas.

Ya ce babu gudu babu ja da baya a matakin da ya ɗauka, sannan ya yi kira ga dukkan ministocin ƙasar su yi abin da ya dace ba tare da cata lokaci ba.

Tinubu ya bayyana haka ne a taron majalisar zantarwa na ƙasar, inda ya yi gargaɗin ɗaukar mataki kan waɗanda suka saɓa umarnin.

“Idan dole kana buƙatar ’yan sanda saboda yanayin aikinka, sai ka yi magana da babban Sufeto Janar na ’yan sanda, sai a nema sahalewa ta,” inji shi.

Shugaban ya buƙaci mai ba shi shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu da ministan ’yan sanda Ibrahim Geidam da shugaban ’yan sanda Kayode Egebtokun su tabbatar an aiwatar da umarnin.

Tinubu ya ce, kariya ga manyan mutane ba aikin ’yan sanda ba ne, inda ya ce ministan harkokin cikin gida Olobunmi Tuni-Ojo zai yi tsare-tsaren maye gurbin ’yan sanda da suke aiki da manyan mutane a ƙasar da jami’an tsaron ciɓil defence, waɗanda an horar domin “ba manyan mutane kariya, kuma suna ɗaukar bindiga.”

By ukarofi