Abin da ya sa janye masu tsaron manyan mutane zai yi tasiri zamanin Tinubu — Alƙali Baba

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsohon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Usman Alkali Baba, ya bayyana cewa dalilin da ya sa matakin gwamnatin Tinubu na janye jami’an ‘yan sanda daga tsaron manyan mutane zai yi nasara shi ne saboda wannan karo umarnin ya fito ne kai tsaye daga shugaban ƙasa, ba daga rundunar ’yan sanda kaɗai ba kamar yadda aka saba a baya.

Baba ya yi wannan bayanin ne a Abuja, yayin ƙaddamar da littattafansa biyu — “Giant Footprints” da “A Policeman Personified” — inda ya yaba wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa ɗaukar matakin da ya daɗe ana tattaunawa a kai amma ba a taɓa aiwatar da shi sosai ba.

A cewarsa, dukkan ƙoƙarin da IGP-IGP suka yi a shekarun baya domin janye jami’an ɓIP ya gagara ne saboda tasirin manyan mutane da kuma matsin lamba daga sassa daban-daban da ke cin gajiyar tsarin.

Ya ce wannan karo bambanci yana nan a fili, domin umarnin ya fito daga matakin siyasa mafi girma — fadar shugaban ƙasa.

“Tun kafin in bar aiki, wannan shi ne karo na farko da irin wannan umarni zai fito kai tsaye daga shugaban ƙasa. A lokacin da nake IGP, mun so mu yi hakan amma abin ya gagara. Yanzu bari mu ga yadda za a aiwatar,” inji shi.

Ya yi ƙarin haske cewa matakin shugaban ƙasa ya nuna ƙwarin niyyar maido da rundunar ‘yan sanda kan ainihin rawar da kundin tsarin mulki ya ɗora mata — wato kiyayewa da tsaron cikin gida — wanda, a cewarsa, ya yi rauni saboda yawan turawa jami’ai ga mutanen da ba su cancanci kariyar manyan mutane ba.

Baba ya ce, wannan umarni ya sake nuna yadda gwamnatin Tinubu ke son farfaɗo da martabar rundunar ‘yan sanda, da gyara yadda ake gudanar da harkokin tsaro domin sake gina amincewar jama’a.

Ya ci gaba da cewa, rubuta tarihin aikinsa cikin littattafan da aka ƙaddamar zai taimaka wajen faɗaɗa tattaunawar kasa kan sake fasalin ‘yan sanda, ya zuga matasa masu tasowa a aikin tsaro, kuma ya ba masu tsara dokoki haske kan ƙalubale da nasarorin da ke cikin tsarin tsaro a Nijeriya.

Wannan jawabi na tsohon IGP ya biyo bayan sanarwar gwamnati cewa shugaban ƙasa ya bayar da umarnin gaggawar janye dukkan ‘yan sanda daga bakin manyan mutane, domin ƙara yawan jami’an da za su koma bakin aiki a yankunan da ke fama da ƙarancin tsaro.

Shugaban kasa ya kuma bayyana cewa daga yanzu, duk wani ɓIP da ke buƙatar rakiyar jami’an tsaro zai koma samun jami’an NSCDC maimakon ’yan sanda.

Gwamnatin ta ce matakin zai sakin dubban jami’an ‘yan sanda domin mayar da su kan ayyukan asali — musamman a yankunan da ke da matsaloli, don ƙara inganta martabar tsaro a ƙasar nan cikin sabon shirin gyaran tsarin ’yan sanda.

By ukarofi