Sakataren APC na Ƙasa ya soki Atiku kan barci a taron Ibadan

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Babban Sakataren jam’iyyar APC na Ƙasa, Ajibola Basiru, ya yi tsokani tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar bayan wani hoto da ya nuna yana barci a taron jam’iyyun adawa da aka gudanar a Ibadan, Babban Birnin Jihar Oyo.

Ajibola Basiru ya wallafa hoton a shafinsa na Facebooka yau Lahadi, inda ya cewa: “Jagoran adawa ya yi barci a wannan muhimmin taron na jam’iyyun adawa.”

Hoton, wanda aka ɗauko daga gidan talabijin na Arise News, ya nuna Atiku Abubakar yana zaune kusa da Kabiru Turaki, shugaban tsagi na jam’iyyar PDP, a yayin taron.

Wallafa hoton ya sa mutane da dama suka yi ta yin martani a shafukan sada zumunta, inda wasu suka yi masa ba’a yayin da wasu kuma suka kare shi.

Wasu sun ce, wannan lamari abin dariya ne, yayin da wasu suka ce yana nuna gajiya sakamakon tarurruka da yake yi ba dare ba rana domin al’umma.

Sakataren APCn ya kuma soki taron, inda ya ce
ba cikakken taron jam’iyyun siyasa ba ne, domin babu sahalewar manyan kwamitocin jam’iyyun da suka halarta.

An gudanar da taron ne a gidan gwamnatin jihar Oyo, wanda ya haɗa manyan ‘yan siyasa da suka haɗa da Peter Obi, Rabi’u Kwankwaso, Aminu Tambuwal, David Mark da Rauf Aregbesola da dai sauransu.

Haka kuma, a taron ne jam’iyyun adawa da suka haɗa da ADC, LP da NNPP suka fitar da sanarwar cewa suna shirin tsayar da ɗan takara guda ɗaya domin fuskantar jam’iyyar APC a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

A nasa ɓangaren, Atiku Abubakar ya bayyana cewa shugabannin adawa sun yi magana da murya ɗaya, yana mai jaddada muhimmancin haɗin kai domin kare dimukraɗiyya a ƙasar.

By Babaji