ACF ta buƙaci ’yan Nijeriya su yi addu’ar sauyin zuciyar ’yan ta’adda

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF), ta yi kira ga ’yan Nijeriya da su rungumi addu’a domin samun sauyin ra’ayi a zukatan ’yan ta’adda, masu ɗaukar nauyinsu da duk waɗanda ke taimaka musu, domin samar da zaman lafiya mai ɗorewa a ƙasar.

Wannan kira na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na ƙasa na ƙungiyar, Farfesa T. A. Muhammad-Baba, ya fitar yayin taya Kiristocin Nijeriya da na duniya murnar bikin Easter na shekarar 2026, tare da kammala azumin Lent da ake yi domin tunawa tashin Almasihu daga cikin matattu.

ACF ta bayyana cewa duk da ƙalubalen tsaro, tattalin arziki da siyasa da ƙasar ke fuskanta, har yanzu akwai fata cewa Nijeriya da yankin Arewa za su iya kaiwa ga samun zaman lafiya, cigaba da kuma kyakkyawar mu’amala tsakanin al’umma.

Sanarwar ta jaddada cewa matsalolin da ake fuskanta sun fi tsanani a yankunan Arewa guda uku na siyasa, inda hare-haren ’yan ta’adda da masu aikata laifuka ke haddasa asarar rayuka, lalata dukiyoyi, tarwatsa al’umma da kuma haddasa rashin jituwa tsakanin jama’a.

Duk da haka, ƙungiyar ta yaba da jajircewar ’yan ƙasa, tana mai cewa yadda mutane ke ci gaba da gudanar da bukukuwan addini duk da waɗannan matsaloli na nuna aarfin zuciya da fata na samun makoma mai kyau.

ACF ta kuma buƙaci dukkan ’yan ƙasa su kasance masu bin doka da oda, su ƙara dagewa da addu’o’i domin dawowar zaman lafiya, adalci da wadata a ƙasar. Haka kuma ta yi kira ga hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi wajen murƙushe ayyukan ta’addanci da laifuka a faɗin Nijeriya.

A ƙarshe, ƙungiyar ta jaddada buƙatar ɗaukar matakan gaggawa da ƙarfi domin kawo ƙarshen ayyukan ’yan ta’adda, tare da fatan cewa za a samu sauyin zuciya a gare su da masu goyon bayansu.

By ukarofi