Sakataren Gwamnatin Tarayya da takwarorinsa na jihohi sun gana a Jos domin ƙarfafa tsarin tafiyar da gwamnati

Spread the love

Daga HABU ƊAN SARKI a Jos

Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ya ƙarfafa buƙatar Sakatarorin Gwamnatocin Jihohi su ɗauki nauyin da ke kansu da matuƙar muhimmanci, a matsayin su na zuciyar aikin gwamnati a jihohin su, domin su ne ƙashin bayan nasarar aikin da gwamnoni ke gudanarwa.

Sanata Akume ya faɗi haka ne a Jos, yayin da yake ƙaddamar da babban taron majalisar sakataren gwamnatin tarayya da Sakatarorin jihohi zango na biyu, wanda ya mayar da hankali wajen tattauna haƙƙokin da ke kan sakatarorin gwamnati, da yadda za su taimaka wajen kawo sauye-sauye, da sauƙaƙa hanyoyin cimma manufofin gwamnati, da tsarin tafiyar da gwamnati.

Sakataren Gwamnatin Tarayya ya kuma bayyana wasu nauye-nauye da ke kan sakatarorin da suka haɗa da tafiyar da hidimar fadar gwamnati, gudanar da ayyukan da suka shafi sha’anin mulki, kyautata hulɗa tsakanin gwamnatin jiha da sauran jihohi da hukumomi, tsara gudanar da ayyukan gwamnati, da kuma ba da shawarwari don inganta ayyukan fadar gwamnati.

Ya nemi da su ƙara neman sanin hanyoyin da za su inganta ayyukan su ta hanyar amfani da fasahar sadarwa ta zamani, da bibiyar abubuwan da ke faruwa a wasu wurare, nuna tsare gaskiya da kiyaye sirrin gwamnati.

Gwamnan Jihar Filato Caleb Mutfwang ya yabawa Sakataren Gwamnatin Tarayya bisa rawar ganin da yake takawa wajen taimakawa gwamnati mai ci da shawarwari, wanda hakan ya yi tasiri ga nasarorin da ake samu a Nijeriya. Ya kuma shawarci sakatarorin jihohin su yi aiki da ilimin da aka koyar da su game da dabarun gudanar da ayyukan tafiyar da gwamnati, domin taimakawa gwamnonin su yadda za su cimma ƙudirorin da suka sa a gaba.

By ukarofi