Daga ALI ABUBAKAR SADIQ
Ya mai karatu, ka sani cewa mai rubutun nan baya bin kowacce irin kungiya a Musulunci, walau Izala, Shi’a, Qur’aniyyun, Darika, Ahmadiyya dss, saboda yarda da na yi da abubuwa guda biyu:
1. Allah ya gargadi Annabi cikin ƙur’ani da cewa; Q6:159 “Lalle ne waɗanda suka rarraba addininsu, kuma suka kasance ƙungiyã-ƙungiyã, kai ba ka zama daga gare su ba, a cikin kõme: abin sani kawai al’amarinsu zuwa ga Allah yake. Sa’an nan Ya bã su lãbãri game da abin da suka kasance sunã aikatãwa.” Kuma duk wanda ya san tarihin musulunci ya san cewa duk wadanan kungiyoyi da muke da su a yau, Annabi da sahabbansa ba su sansu ba.
2. Abu na biyu shine, duk wanda ya yi nazarin daukacin kungiyoyin addinin musulunci, matukar zai yi wa kowacce adalci, hakika zai ga abubuwa masu kyau da marasa kyau a cikin kowacce kungiya.
Wadannan dalilai ya sa na kauracewa kowacce irin kungiya kuma na yarda cewa zan dauki duk wani abu mai kyau, daga duk inda ya bijiro ba tare da la’akari da wanene ya bijiro da shi ba. Haka nan kaucewa duk wata akida mara kyau a duk inda na ji ta. A yau, babu wata kungiyar musulunci mai hadarin Salafiyanci saboda dalilai kamar haka:
Tarihi: Kafin zuwa salafiyya Arewacin Najeriya musulmi na da kungiyoyi daban daban wadanda ke da sabanin fahimta, amma bai hana magoya baya zama lafiya da kuma jurewa sabanin ra’ayi ba. A nan Kano mun ga adawa mai zafi tsakanin Malam Lawan Kalarawi da musammman Sheikh Nasiru Kabara. Kuma daga inda Kalarawi ke wa’azi zuwa gidan Kadiriyya idan ka kwarma ihu za’a jiyo ka. Amma haka Kalarawi zai ta farma Nasiru Kabara da cin mutuncin, amma duk da cewa Nasiru Kabara na da almajirai fiye da kowa a Kano, ba su taba farma wajen wa’azinsa ba.
Zuwan Izala mun ga yadda ta fara haifar da rashin jituwa tsakanin uba da da, yayinda fatawarsu ta haramta durkusawa a gaida iyaye. Gaba ta ruru tsakanin darika da izala. Haka nan Kiristoci da ke zaune a Arewa ana zaune lafiya da su amma zuwan Izala da jefa musu kalmomi irinsu “Arnan banza” ya jawo su ma sun kirkiro “Musulmin banza”. Sannan a shekarun 1980 mu ka fara samun zazzafar adawa tsakanin musulmi da kirista sakamakon da’awa mai zafi irinta malaman Izala, wadda ta kawo kashe-kashe tsakanin musulmi da Kirista.
Tsatstsauran ra’ayi: Ya yi mummunan tasiri tsakanin musulmi a junansu da kuma abokan zama kirista. Ka duba wannan bayani a kasa na wani dan salafiyya mai tsatstsauran ra’ayi game da kisan bayin Allah da ba-su-ji ba ba-su-gani ba a Kaduna su na yin Maulidi. Hujjarsa ka dai ita ce “Yan Bidi’a” ne don haka jininsu ya halatta ke nan ko?
A tarbiya da koyarwar musulunci, rai, ko na kafiri ne, abin tsarewa ne har sai idan ya sabawa shari’a, kuma an tabbatar da laifi. Shi yasa Allah ya ce mana; Q5:32 “…Lalle ne wanda ya kashe rai bã da wani rai ba, ko ɓarna a cikin ƙasa, to kamar yã kashe mutãne duka ne, kuma wanda ya rãya rai, to, kamar yã rãyar da mutãne ne gabã ɗaya…”
Malaman Salafiyya, su na sane ko ba sa sane, sune su ka haifar da tsatstsauran ra’ayi da ya haifar da ta’addanci da sunan musulunci a duniyarmu ta yau. Marigayi Malam Jafar ya taba bayar da fatawar cewa da Musulmi ya zama iri na, wanda baya bin wata kungiyar Musulunci, to gara Dan Bidi’a da shi. Kuma fatawowi irin wadannan masu tsauri da Malam Jafar yayi shekaru gommai a Maiduguri ya na bayarwa ita ta haifar da irinsu Muhammad Yusuf da suka samar da Boko Haram.
Kyamatar nazari da bincike: Kiyayyar da Salafawa ke nunawa yan bidi’a da yan shi’a ko kiristoci da kafirai ba sa nuna musu. Haka kuma kyamatar nazari da bincike a harkokin addini da na zamani shine ginshikin da ya haifar da yan ta’adda kuma yaranmu da dama a yanzu ke komawa mulhidanci. Salafawa sun rungumi Salaf tamkar yadda yan shi’a suka rungumi Ahlul Bayt, ko yan Darika su ka rungumi shaihunnai. Don haka duk abinda su ke zargin wasu, su ma a kai su ke. Wannan ya sa yayinda ake zurawa da gudu mu kuma mu ke zamiya baya. Duk wanda ya zurfafa bincike cikin tarihi zai ga yadda musulmi a baya, sakamakon umarni mafi yawa a cikin ƙur’ani na cewa mu yi nazari, duba, kallo dss ya baiwa musulmin farko kafa harsashen ilimin kimiyya na zamani da Turawa ke tunkaho da shi a yau. Musulmi ne ya fara kera kyamara, jirgin sama, fidar jikin mutum, madubin hangen taurari, na’urar nuna nahiya da inda taurari suke da sauransu.
Amma kyamatar nazarin zamani ya sa daliban salafanci irinsu Muhammad Yusuf sun kona satifiket dinsu sun ce bokon ma haramun ne. Ni kaina na kalubalanci marigayi Jafar a irin wannan akida ta su wadda ta haifar da Boko Haram. A shekarar 2004 an yi husufin rana kuma gidan rediyon Freedom a Kano suka gayyaci Jafar yin bayani kai tsaye yayinda ake wannan husufi. Kalamansa sune cewa turawa karya su ke yi cewar husufi na samuwa sakamakon wata ya shiga tsakanin duniya da rana. Abinda Annabi ya umarce su shine a yi ta istigfari wata ne ke zazzabi. Kuma ya kafa hujja da ayar cikin suratul Yasin da ke cewa: Q36:40 “Rãnã bã ya kamãta a gare ta, ta riski watã. Kuma dare bã ya kamãta a gare shi ya zama mai tsẽre wa yini, kuma dukansua cikin sarari guda suke yin iyo.”
Washegarin wannan husufi, kasancewar a lokacin nima ina gabatar da shiri a Freedom Radio, na yi wa Malam Raddi a cikin program dina kamar haka:
Ita wannan aya ba ta yi karo da bayanan kimiyya na yadda husufi ke faruwa ba, amma dalilin da Jafar ke ganin ta yi karo saboda ba shi da ilimin kimiyya ne. Na bayar da misali da agogon bango wanda ke da hannaye uku, sakan, minti da awa wadanda ke iyo a falaki guda (farantin agogo) amma ba wanda ke shiga hanyar wani. To tamkar haka duniya da wata da rana ke nasu iyon. Amma a agogo duk sanda aka ce sha biyu ta yi, wadannan hannaye na zama a saitin sha biyu, daya a saman daya. Don haka idan hannun sakan da ke sama shine rana, hannun da ke kasansa kuma wata yayinda hannun can kasa ya ke duniya, to tabbas hasken rana zai bugi wata wanda zai kare hasken isa doron duniya don haka sai a ga rana ta shiga duhu. Haka ne yadda husufi ke faruwa, kuma sanin yadda rana, wata da duniya ke motsi ya sa za’a iya sanin a nan da shekaru 100 madu zuwa wacce rana ce za a iya samun husufi (ilimi ne na lissafi ba tsafi ba).
Shi kansa Annabi ya gargadi sahabbai ranar mutuwar dansa Ibrahim, saboda an yi husufi a ranar sai sahabbai su ke cewa ai sakamakon mutuwar ne Allah ke masa ta’aziyya. Nan take ya tara Sahabbai yace “Husufin rana da wata al’amari ne na yadda Allah yayi halitta ba sa husufi don mutuwa ko haihuwar wani.”
Malanta: Haka kuma idan mu ka dubi yadda darajar malanta ta fadi a arewa, tabbas mu zargi irin yadda malaman Izala su ka bada gudunmuwa fiye da sauran malamai. Zuwan gwamnatin Buhari mun ga yadda su ka zake wajen kusantar yan siyasa tare da nuna kwadayi. Mafi muni cikin wannan shine yadda malaman Izala a Kano lokacin badakalar Ganduje suka tafi kwansu da kwarkwata karkashin jagorancin Sale Pakistan da sunan baiwa Ganduje goyon baya bisa zarginsa da ake. Har shi Pakistan ke cewa yadda Allah ya wanke Aisha daga zargin zina hake su ke kyautata zaton Allah zai wanke Ganduje daga zargin Cusa Dollar (Wa’iyazu billah).
Neman suna tsakanin malaman izala ya sa ta kai ga a yanzu sun koma caccakar junansu tsakani Dutsen Tanshi da malaman Izalar Jos. Masu hankali cikinsu, Sheikh Gumi da Pantamj sun fito sun soki lamarin.
Fata na shine a ci gaba da samun Malaman Izala su tashi tsaye wajen yaki da tsatstsauran ra’ayi da kuma assasa fadada tunani wajen nazari da bincike akan al’amuran addini da kimiyyar zamani. Matukar ba a yi haka ba, to matasa masu ra’ayi irin na wannan yaro da ke murnar an kashe mutane babu gaira babu dalili zai ci gaba da karuwa. Mutum ba zai gane irin illar da wannan ra’ayi mai tsauri ke haifarwa musulunci da musulmi ba, sai ya na ta’ammali da wadanda ba musulmi, zai ga yadda ake kara tsanarmu a duniya kuma ake dada raina addininmu. Dole mu hada hannu wajen maido da martabarmu da ta addininmu.
Malam Ali manazarci mazaunin Kano ne
