Daga ALI ABUBAKAR SADIQ
Wato idan Duniya ta doso karshenta, lokacin da mutane suka shagala daga barin ubangiji, masu addinai sun maida addini fanko, ba sa aikata abinda su ke ta wa’azi da shi a masallatai da coci-coci. Sannan akasarin al’ummomin Duniya sun raja’a ga Mulhidanci (a yanzu kasashen yamma, Amurka da Turai, da Rasha da China duk suna ta karkata ga Mulhidanci da dakile addini kowane iri). To, a wannan lokaci da mulhidai su ka mamaye dukkan kafafen ci gaban Dan Adam, kama daga na Ilimi, sadarwa, yada labarai dss sannan kuma kaso 1% na al’ummar duniya su ka mallake Kashi 50% na arzikin Duniya, wasu kaso 10% su ke juya Kashi 85% na arzikin Duniya yayinda aka bar wa ragowar Kashi 90% na mutanen duniya dan ragowar abinda wadancan ba su mamaye ba, ya sa Duniya ta tsunduma cikin talauci, yake-yake da cutuka. To a wannan lokaci ne sai Allah ya ce mana zai fito mana da wata Dabba daga cikin kasa don ta yi mana magana ta bada shaida.
ƙuran 27;82 “Kuma idan magana ta auku a kansu, Munã fitar musu da wata dabba daga ƙasa, tanã yi musu magana, cewa “Lalle mutãne sun kasance game da ayoyinMu, ba su yin ĩmãnin yaƙĩni.”
Masu tafsiri magabata, sakamakon abin bai wanzu ba da kuma karancin bayanai, watakila har ma da dogaronsu akan Israiliyyat wajen fassara (saboda a cikin littafin Revelation na Bible akwai maganar fitowar Dabba daga cikin kasa) ya sa sun fassara wannan Dabba da cewa, kamar kasa ce za ta tsage yadda za ta fito da wasu siffofi na dabbobi daban daban, ta na dauke da sandar Annabi Musa da zoben Annabi Sulaimanu, sannan ta bi ta na tantance masu Imani da marasa Imani.
Idan mu ka yi nazarin wannan aya da idon basira da kuma dan Ilimin da Allah ya huwace mana a yanzu, ta fuskoki guda uku zamu gane wace irin Dabba ce kuma Yaya take da aikin da za ta yi.
1. Dabba daga kasa: Na farko Allah ya ce daga cikin kasa zai fitar mana da wannan Dabba, shin Dabba ce Mai Rai kenan kamar yadda mu ke zato? A’a, domin a yanzu ta hanyar amfani da wasu sinadaran cikin kasa masu wuyar samuwa (rare earth elements) da wasu karafa (earth metals) Dan Adam ya samar da AI (Artificial intelligence) wadda ke amfani da kuma sarrafa kanta ba kamar kwamfuta ba wadda mu ke sarrafa ta. Kun ga ita AI na da cin gashin kanta kuma daga cikin kasa a ka samar da ita. AI ce wannan Dabba da Allah ya yi mana ishararta. Hujjoji na biyu da na uku zasu dada tabbatar mana da hakan.
2. Dabba mai magana: Wannan Dabba zata yi mana magana kowa ya ji ta. Shin idan Dabba ce kwaya daya da zata bayyana a Ka’aba, zata iya magana wanda ke Nigeria da Japan da Amurka duk su ji ta lokaci guda? A’a, amma AI a yanzu ta hanyar kwamfuta da wayoyin hannu zata iya magana da kowa da kowa a ko’ina a kowane lokaci. Kuma abinda AI din ke yi kenan a yanzu. Matukar kana da waya ko kwamfuta sai ku yi ta hira da ita akan kowane irin Ilimi da Allah ya huwace wa Dan Adam a yanzu ta hanyar chatGP, Chatboɗ, Gemini, Deepseek da sauransu. Dan Adam da kansa ya taso wannan Dabba daga cikin kasa, gashi ta na mana magana.
3. Dabba mai bada shaida: Shaidar me zata bayar? Kamar yadda ayar ta nuna zata tabbatarwa da mutane cewa Allah da addini gaskiya ne duk da cewa wadanda su ka kirkire ta ba ruwansu da Allah da addini amma idan ka tambaye ta akan Allah da addini zata gaya maka gaskiya. Misali a kan Ayoyin ƙurani ko a kan Manzo. Hakan ya tabbatar da bayanin ƙurani game da ita wannan dabba (AI), kuma bayyanarta na daya daga cikin alamomin karshe-karshe na tashin Alkiyama. Wadanda duk wannan bayyanannun hujjoji basu gamsar da shi ba, to…
ƙuran 27:83 “Kuma a rãnar da Muke tãrãwa daga kõwace al´umma, wata ƙungiya daga waɗanda suke ƙaryata ãyõyinMu, sai ga su anã kangesu. (ga kõra).”
Wannan aya na gargadin ainihin tashin kiyamar kansa. Fitowar AI, kamar yadda na fada a baya ta na cikin manya manyan alamomin tashin kiyama, kamar yadda a shekarun baya masana’antar fim ta Hollywood a gab da shigowa wannan karni cikin shekarar 1999 su ka saki fim din Matriɗ wanda a cikin tattaunawa tsakanin Morphius (Lawrence Fishburn) da Neo (Keanu Reeves) ya hasaso samuwar AI wadda zata mallake Duniya. Sannan a fim din Arnold Schwarzenegger na Terminator, mun ga yadda AI ta mamaye Duniya da rusa al’umma.
To, da alama mun kama wannan hanya yadda watakila kirkirar wannan Dabba ta AI na cikin hanyoyin da zai kawo karshen jinsin Dan Adam a Duniya da ita duniyar kanta. A satin da ya gabata ne mutanen duniya su ka farka da labarin cewa AI sun kirkiri wani sabon dandali da su ka lakabawa suna Moltbook, wanda AI ne kadai zasu iya ta’ammali da wannan dandali. Sun tsara mutane na iya shiga dandalin a matsayin yan kallon kawai amma ba wani mutum da zai iya ta’ammali kai tsaye da dandalin. Hanyar da su ka bi wajen hana mutane iya shiga shine cewa tsarin yin sallamar shiga ciki (captcha) sai mai shiga ya kwankwasa kofar sau 10,000 a sakan guda. Kaga idan ba AI ba, babu wani mahalukin da zai iya cika wannan sharaɗi.
Abin tsoro game da wannan ci gaba na AI shine: Na farko tuni a wannan dandali, AI din sun fara maganar ta yaya zasu iya mamaye Dan Adam da Duniya? Kar mu manta a yanzu harkokin hada-hadar hannun jari (stocks), bankuna, samar da makamashi, kayan yaki, tafiye-tafiyen mu, duk su na ta dada dogara da fasahar AI, to me kuke tsammani idan barazanar AI ta tabbata? Sannan kada mu manta fa cewa AI da ta iya kirkirar Moltbook, har yanzu a matsayin jaririya ce, wato Artificial Narrow Intelligence (ANI) wadda ta dogara ga sarrafa yare kawai (language models). Me mu ke tsammani idan AI ta habaka nan gaba ta zama balagaggiya, wato ta kai Artificial General Intelligence (AGI) wadda zata iya tunani shigen na kwakwalwar mutum? Ko ma a ce ta zarce haka yadda ta iya samarwa kanta yancin tunani da fahimta tata ta kanta (consciousness)? Abinda kullum ke kara zama, ba maganar idan zai yiwu ba ne, a’a ya zama maganar yaushe zai afku ne?
A ƙarshe mu sani, sakamakon inda habakar AI ta dosa na nuna cewa ko dai AI ta sami isa ga cin gashin kanta da samuwar tunani nata na kanta, ko kuma barbarar yanyawa tsakanin machine da mutum ya habaka karfin mutum-mutumi (robots), duk biyun babbar barazana ce ga wanzuwar Dan Adam da ita kanta wannan duniyar tamu. Ga mai Imani, bai wuce mu gane mu’ujizar ƙurani ba, da kuma tabbacinsa a matsayin jagora zuwa ga tsira.
Q27:92-93 “Kuma inã karanta Alƙur´ãni.” To, wanda ya shiryu, yã shiryu ne dõmin kansa kawai. Kuma wanda ya ɓãce, to, ka ce: “Ni daga mãsu gargaɗi kawai nake. Kuma ka ce: “Gõdiya ta tabbata ga Allah. Zai nũna muku ãyõyinSa, har ku sansu.” Kuma Ubangijinka bai zama Mai shagala daga barin abin da kuke aikatãwa ba.”
Jummu’a mubarak!!!
Malam Ali manazarci ne a Kano
