Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Tun 1966 da su Chukwuman Nzeogwu su ka shekar da jini don ƙiyayyar bambancin addini da ƙabilanci, hakan bai zama darasi ga Buka Suka Dimka ba, cewa yin kisan gilla da kuma karawa da muguwar manufar ƙabilanci ba ya kawo nasara. Dimka ɗan Arewa amma maimakon ya nuna halin dattaku irin na Janar Theophilus Yakubu Danjuma, sai ya jagoranci mutanensa su ka yi kwantan bauna a hanya su ka buɗe wuta kan shugaba Janar Murtala Ramar Muhammad a ranar 13 ga Febrairu 1976 su ka yi ma sa kisan gilla. Na ji ƙanwar Janar wato Hajiya Balaraba Ramat na cewa ta na tuna har a ka binne Janar Murtala a Tudun Maliki nan anguwar Hausawa a Kano, da jini a jikinsa da ya sauka kan makarar da a ka ɗauke shi a kan ta!.
Kaico, juyin mulkin su Dimka ya jawo abin juyayi na zartar da hukuncin kisa a dokar soja kan Dimka, Bisalla, Gomwalk, Tense, Dabang, Mshelia, Dawurang, Gagara da sauran sojoji da ya dace su zama jakadu na gari na Arewacin Nijeriya a Legas.
Dimka na cewa dalilin cin hanci da hargitsa yanayin mulki da sauran su ne ya sa su juyin, amma tarihi ya nuna ba haka ba ne, kawai kyashi ne da rashin haƙuri ga uwa uba biyewa zuciyar ƙabilanci. Duk lokacin ma matasa ne kwarai don Dimka har ya koma ga Allah dududu shekarunsa 36. Ba lallai warshen juyin mulki ba kenan amma ba irin na Dimka ba, don a ranar 31 ga Disamba 1983 sojoji sun kifar da gwamnatin farar hula ta Alhaji Shehu Shagari amma ba kisan gilla. Sojoji su ka ɗora Manjo Janar Muhammadu Buhari. A ranar 29 ga Agusta 1985 Janar Babangida ya zama shugaba bayan kifar da gwamnatin Buhari nan ma ba kisan gilla. Janar Babangida ya sha fama da yunƙurin kifar da shi har mafi rashin kan gado na ƙabilanci da bambancin addini a ranar 22 ga Afrilu 1990 da Manjo Gideon Gwaza Orkar daga Binuwai ya jagoranta, ya yi wuf ya kori dukkan jihohin Arewa na musulmi daga Nijeriya ya yi sanadiyyar kisan gilla ga Kanar UK Bello da sauran dakaru amma yunkurin bai samu nasara ba.
Gaskiyar magana Nzeogwu, Dimka da Orkar su na da hannu dumu-dumu wajen mayar da hannun aggogon cigaban Nijeriya baya don yadda ƙabilanci ya mamaye zuciyarsu da fikirar tunaninsu. A zamanin yau an wayi gari wasu masu kwana su tashi cikin hassada da bakar zuciya sun auka tekun bambancin addini da ƙabilanci su na neman wargaza Nijeriya. Kawai fa su na son cimma muradun samun ƙarfin iko da makudan kudi ne amma ta mummunar hanyar zama a doron addini da ƙabilanci. Ba mutanen Allah ba ne sam. Rashin mallakar jiragen fantamawa a duniya da gidaje a London, Washington da Dubai na damun da yawa daga cikin su.
Miyagun nan na da hannu dumu-dumu a ta’addancin da ke aukuwa kama daga mayaƙan ESN na IPOB zuwa ‘yan ta’addan daji. Miyagu sun ƙirƙiri makircin ruruta kamfen ɗin karya na fakewa da a na danne Igbo don haka dole a bar su, su yi ƙasarsu amma ta hanyar kashe-kashe. Haka nan ma a nan Arewa miyagun su ka kirkiri Hausawan karya masu kunna wutar fitina ta yanar gizo da amfani da sunayen karya don murƙushe Hausawa da sauran al’umma. Kun ga ai har Amurka su ke tafiya su kai labarun karya don a ƙaddamar da yaƙi kan Nijeriya in ya so ko kasar ta wargaje ma ba su da bakin ciki tun da su na tsammanin za a hallaka dukkan waɗanda su ka tsana don kawai ƙabila da addini sun bambanta.
Ba gagga na bayan fage da ke ingiza wutar na fi takaici ba, a’a ƙananan yara da su ka ingiza cikin wannan mummunan aiki da ke yin kamfen ɗin ido rufe kuma a ƙarshe ba riba. Duk mugaye na bayan fage sun ɗan more shekaru da mukaman gwamnmati da ribar rayuwa har ma wasu tsufa ya fara cin mu su, amma yara masu wayar salula fa, a salular za su kare!?
Haƙiƙa makiya Arewa sun cuci ɗaukacin Najeriya don yadda su ke kulle-kulle kan lallai sai an wargaza ƙarfin Lardin da su ke hamayya, don kullum sai an godewa Sir Ahmadu Bello da sauran magabata da su ka sadaukar da hutun rayuwarsu zuwa yi wa yankin hidima. Shi Sir Ahmadu Bello ma har rayuwarsa ya rasa amma bai rasa manufarsa ta shuka alheri gadon barci a wannan ƙasa ba. Sai da na saurari wani faifai dazu na fahimci kwabo da kwabo, irin miyagun kalaman da ‘yan Hausa zalla ke yadawa, tsari ne kai tsaye daga wadannan makiya masu nuna bambancin addini da ƙabila. Ilimin ‘yan Hausa zalla bai kai a bar su, su tsara kamfen ɗin ba, sai dai a yi amfani da su, su yi shigar Hausawa su na yayata wannan manufa, shikenan sun gama aikin su. Dalili na kai tsaye su ke yin kamfen ɗin a ɓoye ta kafafen yanar gizo ba sunan gaskiya, ba adireshi ba hoto ko su zaɓi hoton wani su maka kamar Makau.
Shi Riley Moore a matsayinsa na dan majalisar wakilai daga ɓiginia ta yamma kuma dan jam’iyyar Rifabulikan ta su Donald Trump, kan kai ƙorafin iyayen gidan ‘yan Hausa zalla Amurka, tamkar ɗan majalisar dokoki ne a Abuja da ke da hurumin wannan aiki. Abin farin ciki dai Amurka ba za ta yaƙi Nijeriya ba sai dai Moore da ‘yan kanzaginsa su kawo kalaman ɓatanci marar sa tushe. Jami’an sirri na Amurka sun san gaskiyar abin da ke faruwa a Nijeriya kuma tabbas za su ba da shawarar hanya mafi riba ta tinkarar fitinar.
Shafin Riley Moore na yanar gizo na cike da ‘yan IPOB da ‘yan aƙidar Middle Belt ne fiye ma da ‘yan mazaɓarsa ta ɓirginia ta yamma. Tabbas in Moore a nan Nijeriya ya ke, ‘yan IPOB da ‘yan barandarsu, shi za su zaba, amma yanzu ma ya na fama da sake neman takara kuma a na samun masu cewa e amma wasu na cewa a’a ya daina wahalar da jama’a.
Wallahi in ka ɗebe yarfen jahilci na ribar tallan nono, ’yan cire da zunduma ashar, ba wata manufar farafagandar nan da ’yan karyar Hausa zalla su ka ɓullo da ita, face daukar kalaman miyagun nan da su ka tsara su tun hutun korona bairos, sai kuma karaf zaɓen 2023 na shugaba Tinubu da ya tsaya takara da Kashim Shettima ya zaburar da kamfen ɗin. Ko an yi nasarar ƙona Arewa ba wata riba da ‘yan karyar Hausa zalla za su cimma don a na amfani da su ne kuma an raina iliminsu da shekarunsu ko wayewarsu don akasari yara ne kanana da ba su san ciwon kan su ba. Jahilci na damunsu don waɗanda su ke yaƙar ma, su ne masu taimakon su a rayuwa. Duk wani dan ikirarin Hausa zalla in ya duba zai ga waɗanda ya ke yaka, na da amfani kai tsaye ko a kaikaice ga rayuwarsa ko ma sun sha taimakonsa mma saboda wannan fitina ya bijire!.
Sannu a hankali duk masu hankali sun gane kwangilar ‘yan karyar Hausa zalla ta yaƙi da Musulunci ta na kudundune ne a cin zarafin kowa da sunan Fulani. Ba nan su kan tsaya ba, su kan maida sunan Fulani a matsayin ‘yan ta’adda alhali sun san hakan babban zalunci ne. Abin lura, ba ma su na yaƙi da ta’addanci a Arewa ba ne sam-sam, logar ita ce fakewa da ‘yan ta’addan daji da yi mu su kuɗin goro cewa FULANI ne don zagin Musulmi. Kasancewar ‘yan Hausa zalla ba Hausawa ba ne kuma ‘yan bazata ne, don haka su ka wayance da sunan Fulani a kwangilar yaƙi da Musulmi. Idan kai tsaye sun fito ƙarara sun tinkari Musulmi ba za su samu nasara ba. Ko sunan AGWAI da su ke faɗa ba Kalmar Hausawa ba ne, kalma ce ta kananan ƙabilun Arewa ta tsakiya kan Fulani makiyaya.
Kwanakin baya ‘yan karyar Hausa zalla sun yi ta ruruta kiran a daina bin waɗanda su ka zayyana da limamai Fulani sallah. Makircin a nan shi ne Musulmi da ba Fulani ba, su tada yaƙi a masallatai wajen ture duk limamin da a ke tsammanin Bafulatani ne, daga nan in ta kai ga asarar rai sai ‘yan uwan Fulanin su taho ɗaukar fansa shikenan an haddasa yaƙi tsakanin Musulmi. Wannan makirci bai yi nasara ba, don Musulmi ba sa addini kan doron ƙabilanci. Hausawa a tsakiyar Kano za su bi limami Bayarbe ko Igbo sallah kuma ba tare da tunanin ƙabila ba don a lamarin Musulunci addini shi ke kan gaba da harkar kabila. Kawai musulmi kan yi amfani da ƙabila ne wajen sadarwa a wa’azi, ma’ana ta amfani da yaren da mutane ke ji don kiran su, su karɓi TAUHIDI.
Wannan zayyana ta karya da ‘yan Hausa zalla su ka yi kan Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir ta nuna sharrin su ya kare don a wani hoto da su ka tsara da alamun na AI ne kayan da ma abun hannu na wannan zayyana ba kalar malamanmu ba ne. In hukuma ta cafke masu wannan sharri sai wasu ‘yan bazata su ce an take haƙƙin fadar ra’ayi don rashin sanin me ra’ayi me zunduma karya da ɓatanci. Wadanda su ka yayata hoton nan don cin zarafin Sheikh ba su samu nasara ba. Ai sun fara ne tun kan Shehu Mujaddadi, su ka diro kan Sheikh Abubakar Mahmud Gumi da Sheikh Dahiru Usman Bauchi. Nan ba a maganar sauran malaman Musulunci da su kan kafe hotonsu, su zage su, iya son ran su. Ina kara amfani da wannan dama wajen kira ga duk shugabannin addinan da ba musulunci ba, su ɗau matakan tsawatawa mabiyansu wajen kaucewa neman tada fitinar da ba a san illar da za ta haifar ba. Su kuma masu cin zarafin malaman Musulunci, su sani tabbas ba za su yi nasara ba don sun kama hanyar da ba ta ɓullewa.
KAMMALAWA
Waɗannan ɗabi’u na ‘yan ikirarin Hausa zalla ba na Musulmi ba ne. Ba musulmin kirki da aikinsa shi ne zagin manyan malamai magabata da kushe mumbarin Musulunci amma a waje guda su na kare hatta ɗakin tsafin Barbushe da Tsunburbura. Mutanen nan ba wai don sun san darajar Dutsen Dala ba ne sam, kawai su na amfani da duk wani tarihi waje da musulunci don yaƙi da Musulunci.
