Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Wannan batun ba sabo ba ne. An daɗe ana tattaunawa kan yadda ake satar yara ƙanana ko sayar da su kamar gyaɗa ga masu buƙatar yara a wasu jihohin Kudu. Rahotanni da dama sun tabbatar da yadda aka riƙa sace ƙananan yara masu wayo da marasa wayo, daga gidajen iyayensu, a cikin unguwanni, da kasuwanni, zuwa jihohin Anambra, Inugu, Imo, Riba, Kuros Ribas da kuma Delta, har ma da Jihar Legas. Waɗannan yara da shekarun su ba su wuce 18 ba, waɗanda suka haɗa maza da mata, sun fito ne daga jihohin, Filato, Bauchi, Kano, Gombe, Kaduna, Borno, da Sakkwato.
Idan za ku iya tunawa tun a shekarar 2016 ake taƙaddama kan wasu yara ƙanana da shekarun su basu wuce biyu zuwa goma ba, waɗanda aka sace daga Jihar Kano zuwa wasu jihohin Kudu, waɗanda ake zargi da an sace su ne don a sayar da su ga masu buƙatar yara, ko don su yi aikatau, ko a koya musu karuwanci ana neman kuɗi da su. Ba ƙaramar daga ake ci ba, wajen bincike da gano wuraren da ake kai waɗannan yara da ake sacewa bayan an gudu da su daga jihohin su na asali ba.
Yayin wani bincike da aka gudanar ƙarƙashin rundunar tsaro ta farin kaya, an gano wani gidan marayu na bogi dake garin Asaba a Jihar Delta, inda ake kai waɗannan da sunan marayu ana sayar da su ga masu buƙata. Lamarin da ya kai ga bin diddigin wuraren da aka kai yaran bayan an sayar da su, har ma kuma wata kotu a Jihar Kano ta ɗaure waɗanda ake zargi da hannu a wannan ɗanyen aiki.
Sashi na 30 na Dokar Kare Haƙƙoƙin Yara ta 2003, wacce aka yi wa kwaskwarima a shekarar 2005 da 2015, ya ayyana saye da sayarwa, ko bayar da hayar yara ƙanana a matsayin babban laifi, yayin da sashi na 32 ya haramta amfani da yara wajen yin bara, ko talla, ko wani aikin baɗala da ya danganci karuwanci ko zubar da kimar ɗan adam. Da kuma sanya yara ƙanana yin aikin da ya fi ƙarfin shekarunsu. Kowanne daga cikin waɗannan laifuka, za a iya ɗaure duk wanda aka samu da hannu a ciki shekaru biyar a gidan gyaran hali ko tarar kuɗi da ta kama daga Naira Miliyan ɗaya zuwa Miliyan 5.
Jihar Filato na daga cikin jihohin dake fama da wannan matsala ta safarar ƙananan yara, inda ake sace su a kai su jihohin Kudu ana sanya su karuwanci da aikatau. Sakamakon yadda wannan matsalar take cigaba da ɗaga hankalin hukumomi a jihar, Hukumar Kare Haƙƙoƙin Jinsi ta Jihar Filato tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro sun kai samame wasu gidajen karuwai inda ake ajiye yara mata ana lalata da su don su haifi jarirai da za a sayar, da kuma gidajen da ake lalata da ƙananan yara mata, domin ceto rayuwar waɗannan yara.
Ba sau ɗaya ba, Gwamnatin Jihar Filato, ta sha kama irin waɗannan mutane masu safarar ƙananan yara, ana gurfanar da su gaban shari’a. Ko a shekarar da ta gabata ma, an kama wani da yake iƙirarin shi mai aikin bushara ne, amma yana fakewa da yardar da jama’a suka yi masa, a matsayinsa na mai addini, yana sayar da yaran da yake ajiyewa da sunan taimakon marayu.
Ya zama dole a yaba wa jami’an ƙungiyar direbobi dake kula da wasu tashoshin mota, waɗanda ke taimakawa hukumomi wajen sa ido kan fasinjoji dake zuwa don kai su wasu wurare da ake zargi da harkar safarar ƙananan yara da ƴammata. Wani rahoto da aka wallafa a ƙarshen shekarar da ta gabata, ya bayyana yadda wasu masu kula da lodi a tashar motar Talatu Jang dake Jos, suka kama wasu ƙananan yara biyar da aka je za a tafi da su Kalaba a Jihar Kuros Ribas. Yayin da aka kama wasu yaran daban a wata tashar mota, za a aika da su zuwa Legas ba tare da ɗan rakiya ba.
Wannan babban abin takaici ne matuƙa. Yaya za a yi ka haifi yara, amma saboda talauci ko wahala ka ce za ka sayar da su. Ko ka bayar da su haya wasu na neman kuɗi da su kai ana ba ka na cefane, ba ka san a wanne hali suke ciki ba? A wannan yanayi na lalacewar tarbiyya da tsaro, har wani uba ko uwa za su iya kwantawa barci, ko nuna rashin damuwa da halin da ɗa ko ‘yar su ke ciki?
Wannan mummunar harka na cigaba da zama alaƙaƙai ga hukumomi ba a Jihar Filato ko Kano kaɗai ba, kusan dukkan jihohin Arewa, musamman wuraren da ake fama da ƙalubalen tsaro da matsalar tattalin arziki. Kwamishinan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Filato, Philemon Audu Daffi ya bayyana cewa, “Abubuwan dake faruwa na nuna mana madubin yadda al’umma ta lalace ne. Akasarin waɗannan yara ba a son ransu ake tafiya da su waɗannan jihohin ba, matsaloli ne da suka shafi ƙalubalen tsaro, taɓarɓarewar tattalin arziki, lalacewar zamantakewar iyali, da rashin kulawar wasu iyaye.”
Wata mata a Jihar Filato, mai suna Naomi (ba sunan gaskiya ba ne), ta bayar da ’yarta budurwa domin a kai ta wata jiha a kudancin ƙasar nan da sunan za ta yi aikatau don ta nema musu kuɗi, sakamakon mutuwar mijinta, wanda ’yan ta’adda suka kashe shi a gona. Amma bayan wasu ’yan watanni, suna waya da ’yar tata sai take gaya mata cewa ita ta gaji ba za ta iya zama ba, saboda abubuwan da ake yi mata. Kodayake kai tsaye yarinyar ba ta iya sanar da babarta abubuwan da ake yi mata ba, amma daga bisani bayan ta takura mata da tambaya, yarinyar ta shaidawa babarta cewa, karuwanci ake sa su suke yi kuma ana karɓe kuɗin. Wannan al’amari ya firgita wannan uwa, wacce da kanta ta aika da ’yarta cikin mummunar rayuwa, ba tare da ta sani ba.
Wannan al’amari ba ga yaran Filato kaɗai yake faruwa ba, kuma ba lallai ‘yan matan da ake turawa aikatau jihohin ne ake lalata musu rayuwa ba. Hatta waɗanda ake ɗaukowa daga ƙauyuka zuwa birane neman kuɗi, da waɗanda ke rayuwa a sansanonin ’yan gudun Hijira. Har ma da masu zuwa karatu wasu manyan makarantu da ke nesa da iyayensu, suna shiga harkar karuwanci da sunan neman kuɗin zama a makaranta. Za ka ga ƙananan yara ’yan mata da ba su kai shekaru 18 ba, amma rayuwar su ta zama abin tausayi da takaici.
Lallai akwai buƙatar a ƙarfafa wayar da hankalin al’umma ga makomar rayuwar waɗannan yara, tarbiyyar su, da ilimin su, da kuma rayuwarsu a matsayin su na manyan gobe. Waɗannan yara ne da ya kamata a ce suna makaranta, ko suna ƙarƙashin kulawa da tarbiyyar iyaye, a maimakon yi wa wasu bauta, ko a riƙa lalata da su ana koya musu mummunar rayuwa. Lallai ne iyaye su mayar da hankali ga sauke nauyin da ke kansu na kula da tarbiyyar yaransu, kuma su sani ubangiji zai tambaye su, akan amanar da ya ba su.
Bayar da yaranmu, ko kuma ɗauke su ba da son ran mu ba, a je a sayar ko a tilasta musu wata rayuwa marar tsafta, ba abu ne da jama’a za su naɗe hannu a bar wa gwamnati ita kaɗai ba. Lallai ne sai mun sa hannu an yi tare da mu. Mu cire son zuciya, sakaci, da rashin kulawa. Mu yi abin da ya kamata a matsayin mu na iyaye, da matsayinmu na al’umma, mu tabbatar da ganin an kawo ƙarshen safarar yara ƙanana da ƴammata.
