
Shirin sufuri na kyauta da gwamnatin Jihar Kaduna ke gudanarwa na amfani da motocin masu amfani da iskar Gas (CNG ) ya ɗauki fiye da fasinjoji miliyan 1.4 akan manyan hanyoyi guda huɗu tsakanin watan Yuli zuwa Nuwambar 2025, wanda ya adana wa mazauna jihar fiye da Naira biliyan 1.39 na kuɗin mota, kamar yadda rahotanni suka ruwaito.
Yayin gabatar da bayanan ga manema labarai a Kaduna ranar Alhamis, Kwamishinan Yaɗa Labarai, Malam Ahmed Maiyaƙi, ya ce an gudanar da wannan tantancewar ne domin gano ainihin tasirin tsarin sufuri kyauta da Gwamna Uba Sani ya ƙaddamar, inda alkaluman suka nuna cewa amfanin jama’a ya ninka tsammanin farko.
Maiyaƙi ya ce shirin, wanda aka fara shi domin ma’aikatan gwamnati da ɗalibai, daga baya an faɗaɗa shi domin ya amfanar da dukkan jama’a masu zirga-zirga a kan layukan da aka ware. “Daga 7 ga watan Yuli zuwa ƙarshen Nuwamba, motocin sun dauki adadi mai ban sha’awa na mutanenmu ba tare da an biya komai ba,” inji shi.
Binciken ya nuna cewa a kwata na uku na 2025 wato daga watan Yuli, Agusta da Satumba motocin sun ɗauki fasinjoji 683,650, Kimanin kuɗin haya na waɗannan zirga-zirgar dai ya kai naira miliyan 738.8 wanda zai kasance tanadin kuɗi kai tsaye ga al’umma.
Adadin fasinjoji ya ƙaru a watanni biyu na gaba. Daga watan Oktoba zuwa Nuwamba, motocin sun ɗauki fasinjoji 626,710, daidai da kuɗin haya da aka kauce na ₦667.2 miliyan. A Watan Oktoba kaɗai ya bada fasinjoji 339,530 saboda dawowar makarantu da ƙaruwa a safarar cikin birni.
Ya ce “Jimillar kuɗin da jama’ar Kaduna suka tsira da shi daga waɗannan hanyoyi huɗu ya kai naira biliyan 1.39 cikin watanni biyar kacal,”
Maiyaki, ya kara da cewa alkaluman sun tabbatar da ƙudirin gwamnan wajen rage raɗaɗin tattalin arziki a kan jama’a.
Ya bayyana cewa motocin suna aiki ne a tashoshi 200 a Kaduna, Zariya da Kafanchan, tare da motocin CNG 30 da ke aiki kullum daga karfe 7:00 na safe zuwa 6:00 na yamma. Hanyoyin sun haɗa da: Tudun Wada–Kawo–Rigachikun, Rigachikun–Yakowa–Maraban Rido, Rigachikun–Kasuwa–Maraban Rido, da Rigasa–NEPA Roundabout.
A cewar Kwamishinan, adadin fasinjojin da ake ɗauka a kullum ya kai guda miliyan 18,426, wanda yayi daidai da 294,824 a kowane wata.
Ya ƙara da cewa, kowace mota na yin tafiye-tafiye takwas a rana, abin da ke nuna babban buƙata da karfin aiki.
Maiyaki ya ce amfanin tattalin arzikin shirin ya wuce bayar da sufuri kyauta. Ya ce shirin ya farfado da ƙananan harkokin kasuwanci, musamman ga ‘yan kan hanya da aka taba kawarwa a baya. “Tattalin arzikin Kaduna ya yi rauni lokacin da aka kore dubban ‘yan kasuwa ƙanana. Wannan tsari yana dawo da zirga-zirga da rayuwa a hankali,” inji shi.
Ya kuma jaddada cewa Gwamna Uba Sani ya kawo wannan shiri ne saboda tausayi, ganin halin ƙalubalen tattalin arziki a faɗin ƙasa. “Mai Girma Gwamna yana da damuwa da jin daɗin kowa ma’aikata, ɗalibai, ‘yan kasuwa da talakawa da ke yawon neman abinci kullum,” inji shi.
Duk da cewa ana bayar da sufuri kyauta, Maiyaki ya ce tsarin ya nuna ƙarfin da zai iya samar da riba idan aka dawo da kuɗin haya a nan gaba.
Ya ce gwamnati za ta ci gaba da nazarin hanyoyin dorewar shirin tare da fifita jin daɗin jama’a.
Kwamishinan ya tabbatar da cewa gwamnati na da niyyar ci gaba da samar da sufuri mai lafiya, tsafta da ɗorewa.
Kazalika, ya ce za a fitar da sabbin alkaluman fasinjoji bayan Nuwamba nan gaba, domin motocin na ci gaba da samun yawan fasinjoji.
