Sanata Marafa ya amince da shan kaye, ya ce babu batun zuwa kotu

Ɗan takarar Sanatan Zamfara ta Tsakiya ƙarƙashin Jam’iyyar APC, Sanata Kabiru Garba Marafa, ya ce ya amince ya sha kaye a hannun takwaransa na PDP, Hon. Ikira Aliyu Bilbis.

A jawabinsa da aka yaɗa ranar Litinin, Marafa ya yi alƙawarin ba zai tafi kotu don ƙalubalantar sakamakon zaɓen ba. Saboda a cewarsa, zuwa kotu zai karkatar da hankalin zaɓaɓɓen sanatan daga barin yin aikin da ya kamata, wanda hakan kuwa zai shafi shiyyarsu.

Ɗan siyasar ya yi amfani da wannan dama wajen yaba wa al’ummar Zamfara ta Tsakiya dangane da damar da suka ba shi ta zame musu wakili a Majalisar Dattawa tsakanin 2011 da 2019.

Kazalika, ya yi godiya ga ɗaukacin masu ruwa da tsaki da sauran magoya bayansa game da ƙarfafa masa da suka yi a harkar siyasa.

Yana mai cewa, ya koyi abubuwa da daman gaske dangane da sabon salon siyasar jihar.

Haka nan, ya yi wa Gwamna Bello Matawalle godiya fa mara masa baya da ya yi kan takarar sanata karo na uku.

Har wa yau, Marafa ya nuna godiyarsa ga jam’iyyarsa da zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da Kwamitin Kamfen Shugaban Ƙasa na Jam’iyyarsu bisa damar da aka ba shi na jagorancin kwamitin neman zaɓen Tinubu a Jihar Zamfara.

Ya ce nasarar da APC ta samu yayin zaɓen Shugaban Ƙasa kaɗai ta isa ta nuna ƙarfin jam’iyyar Zamfara.