Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Sabon Sarkin Arewa na Masarautar Kano, Alhaji Dahiru Sa’idu Gidado, ya bayyana cewa naɗin sarautar da Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sunusi II, ya yi masa alama ce ta ƙauna, amana da kuma girmamawa.
Alhaji Dahiru Gidado ya bayyana haka ne yayin ganawa da manema labarai bayan karɓar sarautar, inda ya nuna matuƙar godiyarsa ga Sarkin Kano bisa amincewar da ya yi da shi.
Ya ce, “Wannan naɗi babbar ƙauna ce da aka nuna mini. Ina addu’ar Allah Ya saka wa Mai Martaba Sarki da alheri, Ya biya masa buƙatunsa, Ya ƙara masa lafiya, Ya warware duk abin da ya dame shi, sannan Ya gafarta wa marigayi Ciroma.”
Sabon Sarkin Arewan ya ce tarbiyyar da ya samu tun yana yaro za ta sa ya ci gaba da riƙo da gaskiya, amana, tausayi da kuma hidimtawa al’umma.
Ya ƙara da cewa ba zai kauce daga kyawawan ɗabi’un da aka koya masa ba, yana mai jaddada cewa hidimar jama’a ita ce ginshiƙin sarautarsa.
Alhaji Dahiru Gidado ya bayyana cewa sarautar Sarkin Arewa sarauta ce ta hakimi, inda mai riƙe da ita ke zama kusa da Sarki, yana yi masa rakiya da tarba, tare da wakiltarsa a wasu tarurruka na gwamnati da na al’umma idan buƙata ta taso.
Ya kuma bayyana cewa sarautar Sarkin Arewa sabuwar sarauta ce a Masarautar Kano, wadda aka aro daga Masarautun Hadejia da Sakkwato, kuma mai riƙe da ita yana cikin mambobin majalisar sarki a waɗannan masarautu.
