Sarkin Gobir: ACF ta buƙaci a zurfafa bincike da sauya matakan tsaro

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Ƙungiyar mashawarta na Arewa, ACF tayi watsi da kisan gillar da aka yi wa Alhaji Isa Muhammad Bawa, Sarkin Gobir na Sabon Birni wanda ƴan bindiga suka yi garkuwa da kashe shi a jihar Sakkwato.

Rahotanni sun bayyana cewa, a ranar 18 ga watan Agusta ne aka yi garkuwa da Sarkin tare da ɗansa inda aka buƙaci kuɗin fansa wanda duk da ƙoƙarin da aka yi na samar da abin da suka buƙata, sai da suka azabtar tare da kashe shi.

Cikin wata sanarwa daga Taskar Gizago, ACF ta bayyana rashin jin daɗinta game da al’amarin inda ta yi kira da a gudanar da zurfin bincike tare da sauya jagorancin tsaro na Ƙasa da ke kula da magance matsalolin tsaro don inganta ɓangaren.

ACF ta kuma miƙa saƙon ta’aziyyarta ga ahalin mamacin da abokansa da gwamnatin Sakkwato da Fadar Sarkin Musulmi da kuma al’ummar Sabon Birni game da babban rashin.

Haka kuma, ta buƙaci al’umma ta zauna lafiya tare da yin kira ga gwamnati, hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma da su yi aiki tare wajen ganin ba a karya doka da oda ba.

By Babaji