Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi
Maimartaba Sarkin Kabin Argungu Allhaji Sama’ila Muhammad Mera ya yi kira ga ‘yan siyasa da su haɗa kawunansu don samun ci gaba da kuma amfanin al’umma.
Ya yi wannan kiran be ranar Litinin ɗin da ta gabata yayin da ayarin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen Jam’iyyar APC ya kai ziyarar ban-girma a fadar basaraken.
Da ya ke jawabi, basaraken ya ce ta hanyar haɗin kai tsakanin masana da ‘yan siyasa ne za a iya samun ci gaba mai ɗorewa a cikin wannan jihar.
Ya ƙara da cewa yana da kyau al’umma su kuma su bai wa tsare-tsaren gwamnati goyon baya wanda ta wannan ne za su cimma burinsu na samun romon dimukuraɗiyya a yankunansu.
Tun farko da ya ke jawabi mataimakin gwamnan jihar Kebbi Sanata Umar Abubakar Tafidan Kabi ya ce wannan ayarin ya kawo gaisuwar ban-girma tare da neman tubarrakin wannan masarautar ne a matsayinsu na masu ɗa’a ga iyayensu.
Ya kuma nemi wannan masarautar da ta ci gaba da bayar da shawarwari kamar yadda ta saba musamman wajen tafiyar da tsare-tsaren ci gaban al’umma tare da bayar da tabbacin gwamnatin jihar Kebbi a shirye ta ke da yi aiki da ita kafaɗa da kafaɗa.
