
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Sarkin Katsina, Alhaji (Dr.) Abdulmummuni Kabir Usman ya naɗa Ibrahim Babangida Zakari, babban ɗan marigayi Talban Katsina, Jakada Ibrahim Zakari, a matsayin Talban Katsina.
A wata wasiƙa da ke ɗauke da sa hannun mai martaba Sarkin, wanda ya aika wa sabon Talban, ya tabbatar masa da Sarautar ne bayan rasuwar mahaifinsa wanda shi ke riƙe da matsayin.
Sarkin ya taya sabon Talban murnan samun Sarautar da fatan zai gaji mahaifinsa wajen kyautata wa al’umma da kawo cigaba a jihar.
Mai martaba Sarkin ya kuma bayyana cewa nan bada jimawa ba za a sanya ranar da za a yi naɗin sarautar.
Sabon Talban, mai shekaru 45, babban ɗan kasuwa ne kuma ɗan siyasa da ya taɓa zama ɗan takarar gwamna Katsina ƙarƙashin jam’iyar PDP.
Hakan na zuwa ne mako guda bayan rasuwar mahaifin nasa.
