
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Makonni kaɗan da rasuwar sarkin masarautar Ijebu, Oba Sikiru Adetona, wani babban sarkin gargajiya kuma sark8n Gusau a Jihar Zamfara, Dakta Ibrahim Bello ya rasu.
Sarkin, wanda ya gaji mahaifinsa da ya rasu shekarar 2015, ya rasu ne a Abuja bayan shafe shekaru 71 a duniya.
Kakakin gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya tabbatar da hakan a wata takarda, ranar Juma’a.
Gwama, Dauda Lawal na jihar ya yi jimamin rashin sarkin tare da jajenta wa iyalai da ɗaukacin al’ummar jihar bisa rashin.
Sarkin ya kasance ma’aikacin gwamnati da ya kai matsayin babban sakatare a tsohuwa Jihar Sakkwato da jihar Zamfara.
