
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya caccaki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan abinda ya kira watsi da yankin Arewa, inda ya ce shugaban ya fi mayar da hankali kan gina kudancin Nijeriya ta amfani da albarkatun ƙasar.
Ya bayyana haka ne a wajen taron shawarwari na masu ruwa da tsaki na 2025 da aka gudanar a Kano, ranar Alhamis.
“Bayanai da muka samu na nuna cewa kamar rabin kasafin kuɗi na tafiya zuwa wani ɓangare guda a ƙasar nan.”
Kwankwaso ya kuma zargi jam’iyyar APC da karkatar da albarkatun ƙasa tsakanin ɓangarori biyu na Nijeriya, inda ya ce “Bari in bai wa waɗanda ke ƙoƙarin yin duk mai yiwuwa wajen ɗaukar komai, su tuna cewa wasu batutuwan da muke ciki a ƙasar nan a yau suna da alaƙa da rashin isassun kuɗaɗe da kuma almubazzaranci da wasu ke yi,” inji Kwankwaso
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, ya ce wannan ya sa ake fama da rashin tsaro da talauci da sauransu.
Kazalika, ya bayyana cewa yawancin hanyoyi da ke arewacin suna cikin mawuyacin hali, wasu ma sun lalace – a daidai lokacin da gwamnatin APC ke ci gaba da ware maƙudan kuɗaɗe wa ɓangaren ayyukan more rayuwa a kudancin ƙasar, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.
A ƙarshe, ya buƙaci gwamnatin Tinubu da ta sauya alƙibla domin tafiya da kowa da kuma tabbatar da cewa an raba albarkatun ƙasa yadda ya kamata domin ci gaban dukkan sassan ƙasar.
