Zan ɗauki matakan shigo da ƙarin gwamnonin PDP cikin APC, inji sabon shugaban jam’iyya Farfesa Yiltwatda

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sabon shugaban jam’iyyar APC na Ƙasa, Nentawe Yiltwatda ya ci alwashin ɗaukar matakai masu tsauri a matsayinsa na shugaban jam’iyyar.

Ya bayyana hakan ne a Abuja yayin hira da gidan talabijin na Channels sa’o’i kaɗan bayan naɗa shi a muƙamin a ranar Alhamis.

Ya ce, zai tattaunawa da masu-ruwa-da-tsaki na jam’iyyar akan shawarar da suak dace wajen tafiyar da jam’iyyar cikin tsari tare da kai ta ga nasara.

Ya kuma ce, zai yi koyi da Shugaba Bola Tinubu wajen tafiyar da mulkin ƙasa ta hanyar amfani da matakai masu tsauri, waɗanda a cewarsa hakan shi ne matakin da ya dace wajen cimma nasarori.

Sabon shugaban na APC ya ƙara da cewa zai yi aiki tuƙuru wajen ganin ya janyo ra’ayoyin gwamnonin jam’iyyar adawa ta PDP zuwa ga shiga APC.

Farfesa Yiltwatda ya bayyana cewa zai yi ƙoƙarin ganin ya haɗa kan ƴaƴan jam’iyyar APC domin hakan shi ne matakin cimma nasarorin da suak saka a gaba.

A halin yanzu APC tana da gwamnoni guda 23 a Nijeriya, yayin da kuma ta ke harin samun ƙarin wasu duba da yadda siyasar ƙasar ke cigaba da ɗaukar ɗumi.

By Babaji