Sarkin Maska ya kawo abubuwan alheri a Funtua

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban ƙungiyar cigaban Funtua kwamred Mannir Suleiman ya bayyana haka a saƙon sa na taya Sarkin Maska, Hakimin Funtua Alhaji Sambo Idris Sambo murna cika shekara 30 a karagar mulki.

Ya ce babu shakka Funtua ta bunƙasa ta fanni daban daban musamman cigaba a harkokin kasuwanci da samar da ababen more rayuwa duk a lokacin hakincin Hakimin.

Shugaban ƙungiyar ya bayyana cewa, kasuwanci ya ƙaru da kimanin 80 bisa 100 musamman kan abinda ya shafi kayan masarufi .

Haka kuma an gina manyan tagwayen hanyoyi da gyaran wasu,samar da jami’a da gina sabbin manyan asibitoci da makarantu duk a tsawon lokacin sa.

Duka waɗannan abubbuwan alheri da gwamnatocin baya da na yanzu da suka samar”Sarkin Maska ya taka rawar gani kan waɗannan cigaba da aka sami,”inji Mannir.

Kwamred Suleiman ya jinjina wa hakimin bisa zaman lafiya a tsawon shekara 30 da Funtua ta samu ya biyo bayan shugabanci na adalci da shi Sarkin Maska ke nuna wa a yankin.

“Sarkin Maska yayi iya ƙoƙarin sa wajan tabbatar da zaman lafiya a tsawon mulkin sa,”Inji kwamred Suleiman

By ukarofi