Ranar Jammaje: Mudassiru ƙasim Maryam A Baba da Bello Ibrahim Bily O sun nishaɗantar da mahalarta

Spread the love

Daga MUKHTAR YAKUBU 

Taron ranar Jammaje da aka saba gudanarwa a duk shekara, a bana taron ya gudana wanda kuma za a iya cewa ya zarce na baya da ake shiryawa.

A ranar talata 30 ga Disamba 2025 ne aka gudanar da taron a babban ɗakin taro na Abdullahi Musa da ke harabar Sabuwar Jama’ar Bayero da ke Kano. Taron ya gudana tun daga karfe 10 na safe har zuwa 7 na dare.

Tun da farko da yake jawabi dangane da shirya taron, shugaban makarantar Jammaje Academy, Malam Kabiru Musa Jammaje, ya nuna farin cikinsa dangane da yadda matasa suka karɓi wannan taron wanda a duk shekara ake samun ƙaruwar mutane masu yawa da suke halarta, don haka wannan abu yana da ƙima a wajen matasa.

Ya ci gaba da da cewa “Manufar shirya wannan taro dai shi ne domin a samar da wata mahaɗa da ɗalibai na makarantar Jammaje Academy da su haɗu da juna tare da sauran jama’a da suke bibiyar tsare-tsaren mu daga nesa wanda zuwa wannan taro na ranar Jammaje zai sa su fahimci tsari da kuma yadda Jammaje Academy take tafiyar da ayyukan ta.

Don haka ne ma muka samar da malamai da za su yi jawabai da ya shafi matasa da kuma muhimmancin karatu da rubutu. Don haka shi ma wannan taro, wani darasi ne mai zaman kansa, muna fatan haɗuwar mu ta zama wani sabon shafi na ilmi da kuma ƙara kyautata alaƙa tsakanin ‘yan makaranta da kuma masu sha’awar su zo a tafi da su. Ina yi wa kowa fatan alheri. Allah ya sa a yi taro lafiya a gama lafiya.”

Shi ma da yake jawabi, Dakta Bala Muhammad, ya yi kira ga matasa da su rungumi ɗabi’ar karatu da kuma naci wajen karatun. Ya ce “Ku duba wannan bawan Allah Kabiru Musa Jammaje. Wanda dagewar ce ta zamar da shi haka a matsayin da yake kai a yanzu, don haka ina kira a gare ku matasa da ku tashi wajen neman ilimi da kuma tsara shi yadda za ku ci gajiyar sa.”

Shi kuwa Sanata Shehu Sani a jawabin sa ya tunatar da matasa kan riko da gaskiya, domin ta haka ne mutum zai mori lokacin sa da tunanin sa.

Bayan ya kammala ne sai aka nuna fim ɗin ‘Jamilar Jammaje’ wanda Jammaje Production ya shirya.

Fim ne mai ƙirƙirƙye har na sa’o’i biyiu da yake ɗauke da darasi na muhimmancin amfani da lokaci, domin duk wani lokaci da aka yi wasa da shi, to damar matashi za ta kuɓuce masa. Haka nan an nuna illar rashin ilimi wanda hakan ta sa jarumar fim ɗin ta samu kanta a ciki.

Fim ne da yake riƙe mai kallo wanda har aka gama ana masu kallo suna shauƙin sa ba tare da ya gundure su ba.

Bayan an kammala kallon ‘Jamila Jammaje’ ne aka bada filin ga mawaƙa, inda fitattun mawaƙa irin su Maryam A Bada, Mudassiru ƙasam Abdullahi Amdaz Naziru Magoya Bello Ibrahim Bly’o suka gabatar da waƙoƙinsu.

Taron  ya tashi a daidai ƙarfi 7 na yamma kuma an yi taron an gama lafiya tare da fatan kowa zai koma gida lafiya.

By ukarofi