Maryam Booth ta zama jaruma ta farko da ta ƙulla yarjejeniya da kamfanin Blackville Talents Agency 

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Fitacciyar jaruma a masana’antun Kannywood da Nollywood, Maryam Booth, ta kafa tarihi bayan da ta zama tauraruwa ta farko da ta rattaba hannu da sabon kamfanin kula da hazaka mai suna Blackville Talents Agency Ltd, wani sabon yunƙuri da ke nufin sauya fasalin kula da masu baiwar ƙirƙira a masana’antar nishaɗantarwa ta Najeriya.

An sanar da kaddamar da kamfanin ne a ranar Alhamis, 1 ga Janairu, 2026, inda shugabannin Blackville suka bayyana wannan mataki a matsayin shiga sabon fage na dabaru, domin gano, kula da kuma fitar da jajircewa da hazakar ‘yan Najeriya zuwa kasuwannin duniya.

The Talents Agency by Blackville, kamar yadda aka bayyana, kamfani ne mai cikakken tsari (360°) da ke riƙe da dukkan ɓangarorin sana’ar ƙirƙira da ta shafi harkar nishaɗantarwa, tun daga gano sabbin masu basirar ƙirƙira, ɗaukar nauyi da kula da su, zuwa gina su a ƙarƙashin wata inuwa, da tallata su a matakin ƙasa da ƙasa.

Kamfanin ya ƙuduri aniyar ƙarfafa gwiwar masu fasaha a fannoni daban-daban na ƙirƙira, tare da samar musu da tsayayyen tushe na sana’a mai ɗorewa.

Blackville Talents Agency Ltd reshe ne na Blackville Media Ltd, kamfanin shirya fina-finai da ya yi fice wajen samar da fina-finan da suke amo a duk lokacin da suka fito, kamar ‘Kaka’, da kuma ‘Mai Martaba’, wanda ya kasance fim ɗin da Najeriya ta zaɓa domin waƙiltarta a Oscar na 2025.

Kamfanin na ƙarƙashin jagorancin Prince Daniel, Darakta kuma Babban Shugaba (CEO), wanda aikinsa ya samu karɓuwa da yabo daga masana harkar fim a ciki da wajen Najeriya.

A matsayinta na tauraruwa ta farko da ta rattaba hannu a kamfanin, Maryam Booth ta zo da cikakkiyar ƙwarewa da gogewa. Jarumar ta lashe lambobin yabo da dama, kuma ta shahara a fim ɗin ‘The Milkmaid’, wanda ya kafa tarihi a matsayin fim na farko daga Najeriya da aka kai Oscar a hukumance.

Baya ga fim, Booth ta gina suna a harkokin; ɗaukar hoto da kayan ado (modeling), waƙiltar manyan kayayyaki (brand ambassador), da kuma ayyukan ƙirƙira na zamani da ke fitar da Najeriya fili a duniya.

A ƙarƙashin yarjejeniyar da aka ƙulla, Blackville Talents Agency za ta kula da dukkan harkokin sana’ar Maryam Booth na tsawon shekara guda, tare da waƙiltarta a Najeriya da ƙasashen waje.

Kamfanin ya bayyana Booth a matsayin jaruma mai ladabi, ƙwarewa da kuma baiwa ta musamman, inda ya ce, haɗin gwiwar zai mayar da hankali ne wajen gina, ƙarfafa da sake tsara martabar sunanta domin ɗorewar tasiri a matakin duniya.

Daga ƙarshe, kamfanin ya yi wa Maryam Booth maraba da hannu bibbiyu, yana mai bayyana wannan haɗin gwiwa a matsayin farkon tafiya mai inganci, tasiri da manufa mai kyau, wadda za ta ƙara haɓaka ƙwarewar da baiwar Najeriya zuwa duniya.

By ukarofi